Ganin yadda Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya samu harkar kiwon lafiya a jihar cikin wani hali na rashin kula, nan da nan ya sanya dokar ta-ɓaci a harkar, wanda daga hawansa mulkin jihar ya shiga yin garambawul.
Ba da ɓata lokaci ba gwamnan ya shiga gudanar da ayyukan inganta cibiyoyin lafiyar jihar, inda aka gyaggyara wasu, aka gina wasu sabbi, aka ɗaga darajar wasu, aka kuma sanya kayan aiki a duk cibiyoyin, sannan aka gina wasu manyan asibitoci a duk yankunan jihar.
Cikin shekara guda waɗannan manyan asibitoci masu fama da rashin inganci da rashin kayan aiki da rashin isassun Ma’aikata, wuraren da suka zama masu haɗari ga ɗan adam ya zauna a ciki, amma Gwamna Lawal ya samar da kayan aiki na zamani, samar da ƙwararrun Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya, suka koma abin dogaro ga al’umma bisa inganci da ƙwarewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp