• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Adaidaita Sahu 650 Da Babura 1000 A Sokoto

Ya Yaba Wa Gwamnan Sokoto Kan Samar Wa Matasa Ayyukan Yi

by Leadership Hausa
1 year ago
Sokoto

A ranar Larabar nan ne Gwamna Lawal na Jihar Zamfara ya jagoranci ƙaddamar da rabon wasu babura da A Daidaita Sahu da gwamnatin Jihar Sakoto ta samar.

Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa takwaransa na jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu bisa ƙara samar da guraben ayyukan yi ga al’ummar jihar musamman matasa.

A ranar Larabar nan ne Gwamna Lawal ya jagoranci ƙaddamar da rabon wasu babura da A Daidaita Sahu da gwamnatin Jihar Sokoto ta samar.

Sokoto

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sayo A Daidaita Sahu 500, babura 1,000, da A Daidaita Sahu mai amfani da lantarki guda 150 domin raba wa matasa a faɗin jihar a matsayin wani mataki na ƙarfafa tattalin arziki.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

  • Gwamnatin Tarayya Ta Ce Har Yanzu Tana Biyan Kudin Tallafin Man Fetur 

Sanarwar ta ƙara da cewa, a jawabin da ya gabatar yayin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, bisa wannan gagarumin shiri. Ya ce, “Wannan shiri ne da ya dace, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki sakamakon janye tallafin man fetur da taɓarɓarewar kasuwar canji, wanda ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan.

Sokoto

“Ina kira ga waɗanda suka ci gajiyar wannan shiri da su yi amfani da damar da aka ba su wajen dogaro da kai da tallafa wa iyalansu, da kuma bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin yankin.

“Adaidaita sahun da za a raba, masu amfani da wutar lantarki ne. Suna da muhimmanci idan aka yi la’akari a kan yanayin da duniya ke canjawa a hankali daga amfani da motocin da suka dogara da albarkatun mai. Motocin lantarki suna da kyau ga muhalli da tattalin arziki, idan aka yi la’akari da tashin farashin man fetur.

“Amfani da su a hanyar sufuri zai yi matuƙar tasiri wajen samar da guraben ayyukan yi ga matasa, wuraren cajin su da makanikan da za su samar da kayan gwaran su”

Gwamna Lawal ya ƙara tabbatar da cewa, gayyatar da aka yi masa a matsayin babban baƙo na nuni ne ga kyakykyawan alaƙar da ke tsakanin al’ummar Sakkwato da Zamfara, wanda hakan ke ƙara zamanantar da Nijeriya.

Sokoto

“Tare da tarihinmu, al’adunmu, da tsarin ci gaba, dole ne mu ci gaba da ba da goyon baya da ƙarfafa juna a kowane lokaci don inganta al’ummarmu. Za mu ci gaba da lalubo hanyoyin haɗin gwiwa don gina kyakkyawar makoma ga jihohinmu biyu.

“Da waɗannan kalamai, ina mai farin cikin sanar da jama’a cewa, domin ɗaukakar Allah Maɗaukakin Sarki da kuma amfanin bil’adama, na ƙaddamar da rabon da babura a matsayin ƙarfafa tattalin arziki ga matasa a faɗin Jihar Sakkwato.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025
Next Post
An Tsaurara Tsaro Bayan Fara Shari’a Kan Rikicin Masarautar Kano

An Tsaurara Tsaro Bayan Fara Shari'a Kan Rikicin Masarautar Kano

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025
Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.