Gwanatin tarayya ta dauki matakin gaggawa na dakile yaduwar barkewar kwayoyin cutar kama kafafu da bakin dabbobi da ta bulla a wata gona da ake kiwon dabbobi a Birnin Kudu na Jihar Jigawa.
Ma’aikatar kula da bunkasa kiwon dabbobi ta tarayya, ta bayyana haka ne a cikin sanawar da ta fitar.
- An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
- Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU
Sanarwar ta ce, ma’aiktar ta tura tawagar kwararrun likitoci takwas a karkashin jagorancin, Dakta Adeniyi Adedoyin, Darakta a sashen tsara ayyuka a ma’aikatar zuwa gonar ta kiwon dabbobin da ke Birnin Kudu, domin dakile yaduwar kwayoyin cutar.
Daga cikin tawagar, akwai kuma wasu kwararru daga cibiyar gudanar da binciken kula da lafiyar dabbobi ta kasa (NBRI) da wasu daga ma’aikatar ta kula da bunkasa kiwon dabbobi tare da taimakawar jami’an da ke kula da lafiya dabbobi ta Jigawa da kuma wasu shugabanni daga bangaren Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah.
Tawagar a gonar ta Mallam Alu Agro-Allied da annobar ta bulla, sun gano cewa; kimanin dabbobi 34 ne dauke da alamomin cutar, inda kuma tuni dabbobi shida da cutar ta harba, suka mutu.
Kazalika, tawagar ta kuma dauki alamomin kwayar cutar; domin yin gwajin tare kuma da kaddamar da yin Allurar rigafi ga dabbobin da ake kiwo da ke daura da gonar.
“Wannan matakin da aka dauka na gaggawa, ya nuna yadda ma’aikatar ta mayar da hankali, wajen tabbatar da kare lafiyar dabbobi, duba da cewa; fannin ne da ke kara taimakawa, wajen kara habaka tattalin arzikin kasar,” in ji Adedoyin.
“Ta hanyar aikin hadaka da muke ci gaba da gudanawa, muna kare hanyoyin sana’ar masu yin kiwon ne da kuma kara taimaka wa shirin shugaban kasa na sake farfado da fata, wato na ‘Renewed Hope Agenda’ tare kuma da shirin dabarun bunkasa kiwo na kasa (NLGAS),” a cewar Adedoyin.
Shi kuwa, Jami’i a Cibiyar Gudanar da Binciken Kula da Lafiyar Dabbobi ta Kasa (NBRI) Hussain Ularamu, ya jaddada bukatar a rika kai rahoton bullar duk wata kwayar cuta ga hukumomin da suka kamata tare kuma da adana bayanan kwayoyin cutar, domin daukar matakan gaggawa.
Kazalika, a lokacin kai daukin, ma’aikatar ta wayar da kan Fulani Makiyaya da wasu masu kiwo, kan muhimmancin tabbatar da tsaftace guraren da suke yin kiwon dabbobinsu da kuma lokutan da ya kamata a rika yi wa dabbobin allurra rigakafi.
Su ma, a jawabansu daban-daban, Manajan Kula da Gonar Isa Mohammed Gadama da kuma Shugaban Kungiyar Miyetti Allah reshen jihar, Adamu Kankau, sun yaba wa gwamnatin tarayya kan daukin gaggawar da ta kawo a gonar, inda suka yi alkawarin ci gaba da bayar da hadin kai.
A nasa bangaren, Kwamishinan Ma’aiktar Bunkasa Kiwon Dabbobi na Jihar Jigawa, Salem Abdurrahman, ya sanar da cewa; ma’aikatarsa, ta himmatu wajen gudanar da yi wa dabbobi allurar rigakafi a duk shekara tare kuma da ci gaba da sanya ido, kan bullar duk wata kwayar cuta da ke harbin dabbobi a jihar.














