Makarantar Ittihadil Ummah Alal-Sunnati Muhammadin (SAW) ta Unguwar Hausawa Garin Jiwa dake Abuja, ta gabatar da walimar saukar karatun Alkur’ani mai Girma, inda ta yaye dalibai guda takwai dukkansu dattawa.
Wani abin mamaki da ba a saba gani ba shi ne, a bisa al’ada yara da matasa aka sani ana yi wa iri wannan walima ta saukar karatu, sai ga shi yau kuma wannan makaranta ta yaye magidanta mata masu shekaru dattaku., Wadannan dalibai sun fara ne tun daga babbaku har zuwa fara koyon rubutu, suka kai ga sun rubuta Kur’ani yadda ake yinsa a allo har kuma suka dawo Tajwid suka samu gogewa akan hakan suka samu damar rubutawa karantawa da kuma samun haddar wasu izu daga Alkur’ani da a halin yanzu dai sun dauki aniyar haddar Kur’ani tun daga Bakara zuwa Nasi.
- Manyan Jigajigan ‘Yan Jam’iyyun Adawa Da Suka Sauya Sheka Zuwa APC A 2024
- Tattaunawar Wakilin CMG Da Ministan Harkokin Wajen Iran
Wakilinmu ya samu zantawa da shugaban makarantar Ustaz Yahaya Balarabe Abdullahi Pandogari, ya bayyana nasarar da suka samu a matsayin jajircewarsu da kuma samun hadin kan wadannan dalibai dattawa. Ya nuna muhimmancin ilimi ga dattawa musamman na Alkur’ani a wannan zamani da wasu ke ganin ilimi ne kawai na yara da matasa musamman idan shekaru sun cin musu.
A karshe ya yi kira da shugabanni su ji tsoron Allah cikin amanar jagorancin da Allah ya wakilta su.
Daliban sun taka muhimmar rawa wajen karanta Kur’ani yadda ya kamata tare da ba wa kowane baki hakkinsa, baya ga amsa tambayoyi a fannin Tajwid. Daliban da suka samu nasarar kammala wannan karatu gami da karbar allo mai dauke da zayyana takardar shaida, sun hada da Alhaji Isa Usman, Muhammad Sani Umar, Alhaji Haruna Ibrahim Malam Isa Auwal, Alhaji Yahaya Garba, Malam Zubairu Adamu, da Alhaji Ashafa Khamis.
Wannan makaranta ta Madarastul Ittihadil Ummah tana rassa a Jihohin Kano, Jos a Filato da sauran jihohi inda ta samu nasarar yaye irin wadannan dalibai masu shekaru daga 50 zuwa sama masana kuma mahadda Kur’ani.