Yoon Suk Yeol ya zamo shugaban kasa na farko mai ci da aka taba tsarewa a Koriya ta Kudu bayan da jami’ai masu bincike suka kawar da shinge da karya wayar da ta kange gidan domin su kamo shi.
Ana binciken Yoon mai shekaru 64 ne dai bisa tuhumar tayar da tarzoma a kasar bayan da ya gaza sauya dokokin kasar da na tsarin mulkin soja a watan Disambar 2024 wani abu da ya jefa kasar cikin rudani.
- Ƴansanda Sun Gano Motoci 2 Da Aka Sace A Kano
- Dalilin Rahoton Farfesa Jega Na Bukatar Taimaka Wa Masu Kiwon Kajin Gidan Gona
Da ma dai majalisar dokokin kasar ta riga ta tsige mr Yoon daga kujerar shugaban kasar to sai dai za a iya tunbuke shi daga kan kujerar ne kawai idan kotun tsarin mulkin kasar ta amince da tsigewar.
To amma tsare mista Yoon din na ranar Laraba ya kawo karshen makonni biyu da aka kwashe ana zaman tankiya tsakanin masu binciken da masu tsaron lafiyar shugaban kasa.
Masu binciken dai daga sashen binciken laifukan rashawa da cin hanci sun gaza kama shugaban kasar a ranar 3 ga watan Janairu sakamakon kwashe awanni shida suna tataburza da dakarun shugaban kasar.
Da asubar ranar Laraba ne kuma tawagar masu binciken ta samu dauki ta hanyar kara yawansu inda suka kai mutum dubu daya tare da ‘yansanda suka yi dirar mikiya a gidan shugaban kasar da ke tsakiyar birnin Seol, inda suka yi amfani da tsanuka wajen hawa katangar gidan da wasu manyan motoci da suka yi musu shinge daga tarar da shugaban.
Kuma bayan kwashe awanni, sai hukumomi suka sanar da cewa an kama mista Yoon.
A wani bidiyo mai tsawon minti uku da aka wallafa, mista Yoon ya ce zai bayar da hadin kai dangane da binciken da ake yi masa duk da dai ya ce kama shi da binciken da ake yi masa ba halattattu ba ne.
Lauyoyin mista Yoon sun ce tsarewar ta saba dokokin kasar. To sai dai kotun kolin kasar ta ce tsarewar an yi ne bisa doka.
A yanzu haka dai ministan kudin kasar, Choi Sang-mok ne ke rikon kwaryar jagorancin kasar sakamakon tsige mataimakin shugaban kasar na farko, Han Duck-soo da majalisar dokokin kasar – da ‘yan hamayya suke da rinjaye, ta yi
Wace dama Yoon ke da ita?
Bisa tsarin sammaci, masu binciken ka iya rike mista Yoon har tsawon awanni 48, kuma daga nan ne suke bukatar samun sabon sammaci na ci gaba da tsare shi domin ci gaba da bincike.
Idan aka samu wannan sammaci, to za su iya ci gaba da tsare shi har tsawon karin kwana 20 kafin a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Idan kuma ba a samu sabon sammacin ba to dole ne a sake shi bayan karewar awanni 48 din.
Magoya bayan mista Yoon dai na ci gaba da gudanar da zanga-zanga domin nuna kin amincewarsu da kamun nasa.
Sun yi dandazo a gaban gidansa tun kafin asubahin ranar Laraba, inda suka kasance daura da masu hamayya da shi.
Waiwaye
Kasar Koriya ta Kudu dai ta yi fama da matsalolin siyasa tun bayan da sanar da sauya dokar kasar da ta mulkin sojoji a ranar 3 ga watan Disamban 2024 wanda ya janyo ‘yan majalsiar dokoki suka tsallaka katanga yayin shiga majalisa domin kin amincewa da dokar.
Shugaban ya ce yana kare kasar ne daga wasu mutane da ke kishiyantar kasar da ke goyon bayan Koriya ta Arewa, amma kuma ba jimawa sai ta bayyana cewa burinsa na siyasa ne ya haifar da hakan.
Shi dai Mista Yoon ya kasance shugaban kasan da ba shi da katabus tun bayan da ‘yan hamayya suka lashe babban zaben kasar da aka yi a watan Afrilu da gagarumar nasara.