Yanzu haka kotun sauraron korafe-korafen zabe da ke zamanta a Jihar Kano ta mayar wa da Jam’iyyar APC kujeru uku daga cikin kujerun da ta kalubalantar Jam’iyyar NNPP mai mulki da mallakarsu tun da farko.
Shara’ar zabe dai a Kano ta fara daukar sabon yanayi, inda tun a cikin makon da ya gabata kotun ta karbe kujerar wakilin karamar Hukumar Tarauni, wanda a farko aka ayyana Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ta lashe zaben. Sai dai sakamako bai yi wa Jam’iyyar APC dadi ba, dan takararta Honarabul Hafizu Ibrahim Kawu ya garzaya gaban kotu, inda ya kalubalanci rashin sahihancin sunan da dan takarar Jam’iyyar NNPP ke amfani da shi. Sakamakon wannan korafin, bayan sauraron bangarorin biyu, kotun ta yanke hukuncin mayarwa da Honarabul Hafizu Kawu wannan kujera.
Haka zalika, kotun ta sake karbe kujerar wakilin kananan Hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam, wadda dan Jam’iyyar NNPP aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben. Wanda ya yi wa Jam’iyyar APC takara, Honarabul Musa Iliyasu Kwankwaso ya garzaya kotu, inda ya zargi cewa dan takarar NNPP bai aje aikinsa ba kamar yadda dokokin hukumar zabe suka gindaya. Hakan ya sa kotun duba hujjojin da lauyoyin bangaren masu korafi suka gabatar, sannan kuma ta yanke hukuncin mayar wa Musa Iliyasu Kwnakwaso na Jam’iyyar APC a matsayin halastacen wanda ya lashe zaben.
Ita ma kujerar karamar Hukumar Kumbotso wadda tun farko aka ayyna Honarabul Idris Dan Kawu a matsayin wanda ya lashe zaben. Kotun sauraron korafe-korafen zaben ta kwace wannan nasara, inda ta tabbatar wa Honarabul Manniru Babba Dan Agundi a matsayin wanda ya lashe zaben tare da cin tarar Idris Dan Kawu naira 200,000.00 ko zaman gidan gyaran hali na watanni shida.
Zuwa yanzu jam’iyyar adawa ta APC ta samu nasarar karbe kujeru uku daga cikin kujerun da suke kalubalantar jam’iyyar NNPP kan ikirarin lashe zabensu, yanzu dai ko shakka babu kallo ya r koma sama, domin bisa ga dukkan alamu wankin hula na neman kai jam’iyya mai mulki ta NNPP dare, ta yadda ake masu dauki dai-dai a kujerun da suke ikirarin lashewa. Wanda kuma har yanzu akwai sauran wasu masu yawa da suke gaban kotu da jam’iyyar APC ke kalubalantar nasararsu.
Wanann hali da jam’iyyar NNPP ta tsinci kai a ciki ya sa wasu magoya bayanta fara sun tunanin me jagororin jam’iyyar NNPP ke ciki zuwa yanzu da suka zuba ido ana ta yi masu dauki dai-dai. Sannan wasu na ganin daman ‘yan takarkarun na Jam’iyyar ta NNPP ba a yi masu taza da tsifa ba kafin tsaryar da su takarar. Wannan ta sa a ganin wasu suke zargin daman ba mamaki an yi kitso da kwarkwata. Baya ga wannan ita Jam’iyyar NNPP daman a Jihar Kano kadai take da adadin kujerun da suke tinkaho da su kuma wasu na ganin takun sakar da jagoran darikar ta Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi da wasu shugabanni masu rike da madafun iko ya kara haifar wa da jam’iyyar tarnaki.
Yanzu dai masu fashin baki na ganin wannan karbe kujerun da jam’iyyar adawa ta APC ke yi na zaman wata ‘yar manuniya da ke haska hukuncin kotun da ake sauraron shari’ar da ake yi tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma Dakta Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC, wanda a iya cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.