Lokaci bako! Kamar yau muka yi bankwana da shekarar 2023, ga shi a wannan karon muna bankwana da 2024 tare da murnar shigowar 2025.
Dama-dama a ce, sauran al’ummatai da shugabanninta za su yi koyi da al’ummar Sinawa da shugabanninta musamman na Afirka, wajen himma da jajircewa da za ta kai ga samun sauye-sauye da nasarori a nahiyar kamar yadda al’ummar Sinawa da shugabanninta ke da himma wajen kawo sauyi domin samun nasara a kasarsu da duniya baki daya.
- Fargabar Hare-Haren Bello Turji Ta Tilasta Mutane Tserewa Daga Yankunan Sakkwato
- Dokar Haraji Za Ta Ƙara Jefa Al’umma Cikin Talauci – Gwamnatin Kano
A ranar jajibirin shekarar nan ta 2025 ne, shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya yi jawabin maraba da sabuwar shekara ta kafar yada labarai ta CMG, inda ya zayyano wasu muhimman ayyuka da kasarsa ta samu nasarori a kan su, kuma duk a cikin shekarar 2024, wannan ya cancanci yabo kuma ya zama abin fata da koyi ga sauran shugabannin duniya musamman na Afirka.
Shugaba Xi Jinping ya bayyana yadda Sin ke cin moriyar amfani da cikakkun tsare-tsare na manufofi don samun ci gaba mai karfi da juriya da hakan ya haifar nasarori.
Tattalin arzikin Sin ya habbaka sosai, inda ake sa ran ma’aunin tattalin arzikin (GDP) kasar zai wuce yuan tiriliyan 130. Yawan hatsi ya haura tan miliyan 700, sannan kuma rumbunan ajiyar abincin kasar cike yake da hatsi wanda mafi yawanci girbin kasar ne (Hatsin Sinawa).
A karon farko, kasar Sin ta kera sabbin motoci masu amfani da makamashin lantarki fiye da miliyan 10 a cikin shekara guda. Haka kuma, a karo na farko na’urar bincike ta Chang’e 6 ta tattaro samfurori daga duniyar wata a yanki mai nisa, kana babban jirgin ruwan binciken teku na Mengxiang ya gudanar da bincike a sashen teku mai zurfi, kuma hanyar da ta ratsa teku mai hada biranen Shenzhen da Zhongshan na taimakawa ga saukaka harkokin sufuri, kuma an kara raya tashar bincike ta Qinling dake yankin Antaktika, al’amuran da suka shaida babban buri, gami da kwazon Sinawa na raya harkokin da suka shafi sararin samaniya da teku.
Bugu da kari, a cikin shekarar 2024, ’yan wasan kasar Sin sun nuna bajinta a gasar Olympics da aka gudanar a birnin Paris, lamarin da ya nuna yadda Sinawa ke cike da himma da kwarin gwiwa na kiyaye kimar kasarsu. Rundunonin sojin ruwa, da na sama na kasar Sin sun yi bukukuwan murnar cika shekaru 75 da kafuwa. Kai! Wani lamari ma mai cike da sha’awa da ban mamaki shi ne, lokacin da ambaliyar ruwa da guguwa da sauran bala’o’i suka afku a kasar, mambobin jam’iyyar kwaminis mai mulki ta kasar da jami’ai sun tashi tsaye wajen jagorantar ayyukan bayar da agajin gaggawa. Lallai wannan ya nuna cewa, Sinawa “tsintsiya daya ce madauri daya”, kuma a kowanne fanni suna aiki tukuru don cika burinsu.
Kasar Sin a matsayinta na babbar kasa mai cike da tattalin arziki. Tana kan gaba wajen ganin an yi gyare-gyare a harkokin mulkin duniya domin ganin cewa, an tafi da kowa da kowa ta hanyar zurfafa hadin kai da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, bisa shawarar “hanya daya da ziri daya”, da tsarin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), BRICS, APEC da G20.
Kasar Sin na samun nasarori ta bangaren hadin gwiwar ci gaba a tsakanin kasashe, inda take ci gaba da taka rawa wajen bai wa duniya zaman lafiya.