Tun bayan kaddamar da tashin maniyyata da aka yi a Jihar Kebbi, sai babban birnin tarayya Abuja ta karba inda maniyyatan Jihar Nasarawa suka tashi zuwa kasa mai tsarki sai kuma jihohin Legas, Bauchi, Kwara suka shiga sahu. Zuwa ranar Laraba 22 ga watan Mayu an samu nasarar jigilar maniyyata 13,070 zuwa kasa mai tsarki a sawu 31 da aka yi.
Yayin da aka shiga mako na biyu da fara jigilar maniyyatan, jihohin Kaduna Yobe Kano, Adamawa, Borno da Sakkwato za su shiga sahu daga ranar Alhamis 23 ga watan Mayu.
- Hajjin 2024: Ranar 10 Ga Watan Yuni Za A Kammala Jigilar Maniyyata – NAHCON
- Ba Za A Yi Gagarumin Bikin Cikar Gwamnatin Tinubu Shekara Ɗaya Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai
Sabon tsarin da hukumar Saudiya ta bullo da shi a wannan shekarar shi ne, kwanaki hudu kacal aka yarje wa maniyyaci ya yi a birnin Madina maimakon kwanaki 10 zuwa sama a shekarun baya. Hukumomin Saudiyan sun bayyana cewa, sun yi haka ne domin rage cunkoso a birnin Madina da kuma barin al’umma masu ziyara su sakata su wala a dan lokacion da za su yi a garin na Madina. Abin nufi a nan shi ne da yawa daga cikin maniyyata daga Nijeriya da suka fara isa kasa mai tsarki sun riga sun kammala zaman su a Madina a halin yanzu sun kuma kama hanyar zuwa Makka inda ake sa ran za su yi Umara su kuma ci gabatar da ziyarori da sauran ibadu har zuwa lokacin da aikin hajji zai kankama.
Wakilinmu zai shiga lungu da sako tare da bin diddigin halin da alhazai ke ciki a Madina, Makka, Mina, Muzdalifah da filin Arfa domin kawo muku rahottanin abin da ke gudana. Muna addu’ar Allah ya ba mu nasarar wannan aikin da muka sa a gaba. Allah kuma ya sa a yi aikin hajji karbabbiya, Allah ya kai mana alhazanmu ya kuma dawo mana da su gida lafiya. Ga wasu rahottanin da muke da su a wannan makon.