Sama da shekaru dari tun bayan da ’yan gurguzu suka kafa jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ko JKS, jam’iyyar ta ci gaba da bunkasa zuwa mafi girma a duk fadin duniya. JKS ta bunkasa daga membobi kimanin 50 a lokacin kafuwarta zuwa membobi sama da miliyan 100 a yanzu.
Tarihi ya shaida yadda JKS ta zamo ja gaba, wajen bayar da kyakkyawan jagoranci ga al’ummar Sinawa, zuwa matakin sauyi mai nagarta, da tabbatar da walwalar al’ummar kasa. Tabbas JKS ta fadada a dukkanin fannoninta, kama daga akidu zuwa manufofi, ta zamo garkuwa ga ’yan kwadago da jama’ar kasar baki daya, yayin da har kullum take kokarin mayar da bukatun al’umma gaban komai.
- Dangote Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Ababen More Rayuwa A Nijeriya
- EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi
Wannan ci gaba ya shaida yanayin musamman na JKS na gudanar da sauye-sauye, da garambawul sabanin jam’iyyu da dama da tarihi ya kiyaye wanzuwarsu. Kazalika, JKS tana ta kokarin cika burinta na dinke dukkanin sassan kasar Sin waje guda.
Tun farko kafuwar jam’iyyar, ta zama wani ginshiki mai nafarta na neman samar da farin ciki ga al’ummar Sinawa, da fafado da kasa, da cimma burika da kudurorin ci gaba. A bangaren yaki da fatara kuwa, JKS ta yi nasarar jagorantar aikin tsamo daukacin ’yan kasar daga matakin talauci matsananci, ta hanyoyin raya tattalin arziki, da samar da ababen more rayuwa da na walwalar jama’a.
Miliyoyin al’ummun kasar Sin sun yi hadin gwiwar shiga yakin fatattakar fatara a sassan kasar. Matakin da ya kai wasu ’yan jam’iyyar da yawansu ya kai 1,800 rasa rayukansu a fagen yaki da talaucin da aka aiwatar. Kazalika, haka ma abun yake lokacin da aka sha fama da annobar COVID-19, inda nan ma sama da ’yan jam’iyyar ta kwaminis miliyan 7 daga jami’an gwamnati, da ma’aikatan kamfanoni, da hukumomin al’umma suka tunkari wannan annoba kai tsaye, duka dai da nufin bautawa al’umma bisa sadaukarwa.
Har ya zuwa yanzu, ’ya’yan JKS na ci gaba da nuna kyawawan misalai a fannin yayata manufar samar da ci gaba mai inganci, da kyautata jagoranci tun a matakin farko, da sauke nauyin dake wuyansu, da gudanar da ayyuka masu cike da kalubale, wanda hakan ya zamo kashin bayan ingiza nasarar jam’iyyar da ma kasar Sin baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp