• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Kamfanin Huawei Na Sin Ke Fadada Moriyar Fasahar Sadarwa A Tanzania

by CMG Hausa
3 years ago
Huawei

Sanin kowa ne cewa a zamanin yau, daya daga muhimman fannonin da ke ingiza ci gaban duniya shi ne fannin fasahar sadarwa, wanda karkashinsa, alummun duniya ke cin gajiyar musayar bayanai da sakwanni ta kafofi daban daban, ciki har da na wayar salula da yanar gizo ko intanet. Hakan ne ma ya sa a kasashe masu tasowa da dama, gwamnatoci ke kara azamar samar da manyan ababen more rayuwa a wannan fanni.

A yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin na kara samun manyan nasarori a fannonin fasahar sadarwa ko ICT, matakin da ke kara ingiza ci gaban tattalin arziki da zamantakewar alummunta a dukkanin bangarori. Kuma kamfanonin kasar masu ruwa da tsaki suna kara taka rawar gani wajen fitar da fasahohinsu ga kasashen waje, ta yadda daukacin alummun duniya za su kai ga cin gajiya daga hakan.

  • China Ta Musanta Daukar Nauyin Ta’addanci A Nijeriya

Kamfanin Huawei mai gudanar da ayyukan raya fasahohin sadarwa na zamani na kasar Sin, daya ne daga manyan kamfanonin duniya da suka yi fice a wannan fage. Inda ko da a farkon makon nan ma ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar fadada turakun samar da hidimar yanar gizo a kasar Tanzania.

Bayan kammalarsa, aikin wanda aka yi wa lakabi da NICTBB, zai samar da hidimar yanar gizo ga gundumomin kasar 23 dake kasar ta gabashin Afirka.

Tuni dai kamfanin na Huawei ya tabbatar da shirinsa na yin aiki tare da tsagin Tanzania, wajen ganin an cimma nasarar kafa manyan ababen more rayuwa da za su warware kalubalen da kasar ke fuskanta a fannin sadarwar yanar gizo, matakin da ko shakka babu zai bunkasa fannin fasahar sadarwa a kasar.

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

A bangaren gwamnatin Tanzania kuwa, manufar wannan aiki na NICTBB shi ne hade dukkanin yankunan kasar da hidimar yanar gizo. Baya ga haka, aikin zai iya taimakawa Tanzania samun damar dunkulewa ta fuskar hidimar fasahar sadarwa da kasashe makwaftanta, kamar Zambia, da Malawi, da Kenya, da Uganda, da Rwanda, da Burundi.

Lura da wannan manufa, muna iya cewa kamfanin Huawei na kasar Sin na taka rawar gani wajen bunkasa fasahar sadarwa a kasashen Afirka, yayin da kasashen nahiyar ke fafutukar samun ci gaba a wannan muhimmin fanni, mai ba da damar bunkasa tattalin arziki da kyautata jin dadin bil adama. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Da Dumi-Dumi: Sarkin Musulmi Ya Ayyana Juma’a A Matsayin Ranar Sallah

Da Dumi-Dumi: Sarkin Musulmi Ya Ayyana Juma'a A Matsayin Ranar Sallah

LABARAI MASU NASABA

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.