Ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya fiye da 746 suke mutuwa, sanadiyar cutar kansar Baki ko wace shekara.
Haka abin yake yayin da ana gano mutane1146 na kamuwa da cutar ko wace shekara.
- Nijeriya Ta Sanya Hannu A Yarjejeniyar Amfani Da Fasahar Shuka Itatuwa Da Kasar Netherlands
- Ina Neman Gafarar ‘Yan Nijeriya Idan Na Muku Ba Dai-dai Ba —Buhari
A wani bayanin da ta fitar a wurin taro na kwana daya mai taken: ‘Amfani da kyakkyawar kulawa tun farko wajen gane ita kansar Baka da yadda take tasiri,’ wadda gidauniyar cutar dajin Baki da nakasar fuska a Abuja makon daya gabata, Ministan ya nuna rashin jin dadinsu yadda mutane da yawa basu san yadda cutar kansa Baka take samar da babbar matsala.
Ya cigaba da byanin “Cutar kansar Baka babbar matsala ce domin tana iya bata fuskar mutum,ba zai iya magana ba, ko ma cin abinci,da yawan mutuwar da ake yi sanadiyar cutar.Ta ma fi sauran nau’oin cututtuka masu nasaba da kansa kamar yadda Ministan yace,” .
Shugaban sashen kulawa da sashen kudi ta ma’aikjatar lafiya ta tarayya, Dokta Gloria Uzo-Igwe,Ministan ya bayyana cewa ma’aikatarsa tana iyakar kokarinta wajen fadakar da ‘yan Nijeriya akan hadarin dake tattare da cutar kansar Baka.
Ya ce an kammala dauka matakan da suka kamata maganar kaddamar da tsari kan cutar kansar Baka.
“Muna da tsarin da zamu kaddamar a watan Nuwamba mai zuwa kan cutar kansar Baka matakin mu shine yana yaduwar cutar, za mu ziyarci al’umma domin wayar da kansu.”
Kowa ya nason ya tafi Birni babu wasu Likitocin hakora a kauyuka babu kwararru a can inda kansar Baka take da yawa.
“Muna zuwa kuyuka mu horar da jami’anmu domin hakan zai sa su lura da alamun duk wanda ya kamu da irin cutar ta kansa,daga nan sai su yi masu bayani su je asibitocin da zasu samu taimakon na kulawa da su.
“Bamu son al’amarin ya kai ga zuwa ga mataki na hudu ko ma na ukun,mudddin za su iya gane su wanda ya kamu da cutar su tura shi asibiti domin daukar matakin daya dace ba tare da bata lokaci ba”
Dokta Osagie ya kara jaddada cewa manufarsu ce a samu akalla kashi 50 na al’ummar karkara da kuma tabbatar da akwai kwararru a asibitocinmu na karkara.
“Manufarmu ce daukar matakin daya kunshi kulawa da marasa kamar yadda ya dace a kalla a ce akwai asbibitin Hakora da zai kunshi kwararr,mai ilmin kwantar da hankali, sai kuma mai kula da tsafta,a kalla a shiyyoyi uku na kasa.
Da yake na shi jawabin wanda ya kira atron na horarwa Dokta Bello Alokun,ya ce akwai wani tsari na amfani da komfutoci,inda bayanan da aka samu wurin mara lafiya za a iya amfani dasu kashi 90 na ainihin gaskiyar da za a iya gane cewar shi mutumin zai iya kamuwa da kansar nan da shekara goma.
Kamar yadda yace matakin zai “ taimakawa su kwararrun su sa ido domin lura da irin mutanen yadda da hakan zasu gane shiga cutar tuna bin bai yi nisa ba,hakan ne kuma zai bada dama ta maganin kansar da mutumin yake fama da ita.
“Shi tsarin da ake son amfani da shi ana son ya kasance matsayin gwaji inda amfaniun shi za a iya amfani da shi ta bangarori daban- daban na magunguna da kuma sauran al’amarin da ya shafi kimiyya.Nijeriya tana gab da cimma burin haka nan.
“Muna kokarin yadda za a fadada tsarin lokacin da za a iya kamuwa da cutar kansar Baka da bada labarin ga ‘yan Nijeriya ta yadda za a iya kamuwa da cutar saboda gane kamuwa da ita cutar wani muhimmin al’amari ne.”
Ita ma a tata gudunmawar Farfesa Bukola Folashade Adeyemi ta Kwalejin jami’ar Ibadan ta bayyana cewa duk da yake kansar Baki bata faye yawa ba a Nijeriya amma duk da haka tana da matukar hadari.
“Ba ina nufin dole sai mutanen da suke da nasaba da abubuwan biyu suke iya kamuwa da cutar Kansar Baki ba, akwai mutanen da suka gada daga cikinsu suna iya kamuwa.
“Abinda muke ba mutane shawara shine su guji hada kansu da ko wata mu’amala da abubuwan biyu.Wannan zamanin ma wasu matasa sun kara gyara kan shi al’amarin yadda suke amfani da abinda ake kira a zamanance e-smoking,suna ma amfani da wani abu da ake kira da suna shishar da sauran abubuwan da suke da matukar hadari ga rayuwarsu.
“Namu shi ne mu ba mutane shawara su kaucr ma hanyar ko halaiya irin wadda bata dace ba.”
Da ta cigaba da yin karin bayani sai tace rayuwar da muke a wuraren da muke zama shine yawan amfani ko cin kayayyakin abincin da ake yin amfani da wutar da za a gani a zahiri wajen sarrada su kafin a ci, musamman ma ga mutanen da dole kullun sai sun kasance a irin halin ko yanayi.