Daya daga cikin manyan kudurorin kasar Sin na zurfafa binciken kimiyya da fasaha da ta sanya a gaba shi ne batun gina tashar bincike a sararin samaniya domin mayar da hankali a kan yadda za a ci gajiyar albarkatun duniyar wata yadda ya kamata.
Domin cimma wannan kuduri, kasar Sin za ta aike da kumbon bincike na Chang’e-7 a shekarar 2026 domin gano yanayi da albarkatun da ke yankin kudancin duniyar wata. Kana a shekarar 2028, za ta sake kaddamar da aikin binciken da kumbon Chang’e-8 zai yi a kan yadda za a sarrafa albarkatun duniyar wata.
Ana sa rai nan da shekarar 2035, wadannan bincike-bincike da kumbunan za su yi za su samar da fahimtar yadda za a gina tashar binciken duniyar wata ta kasa da kasa ta gwaji kamar yadda hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta bayyana.
Hakika kasar Sin tana ci gaba da nuna wa duniya kwarin gwiwa game da ci gaban ilimi da fasahar bil’adama wajen cin gajiyar albarkatu ba kawai a wannan duniyar da muke rayuwa a doron kasa ba har ma da sararin samaniya.
Kasar Sin ta jajirce kan wannan aikin saboda masana sun ce, yin gini a duniyar wata yana bukatar kyakkyawan nazari wajen zabo wurin da ya kamata a gina, da kayan ginin da za a yi amfani da su. Ana bukatar filin da za a yi ginin ya zama shimfidadde mara tudu da gangare domin kumbuna su rika sauka ba tare da tangarda ba, sannan wajibi ne ya zama mai saukin sha’ani wajen sadarwa tsakanin duniyar wata da doron kasa, kuma ya kasance mai jure wa yanayin lokacin yini da na dare na duniyar wata wanda kuma har ila yau yake samun isasshen hasken ranar da ake bukata, kana ya zama akwai albarkatun ruwa da kankara a kusa da inda yake.
Kasar Sin ta zage damtse kan wannan aiki inda ta kuduri aniyar yin ginin tashar da kayan da aka sarrafa da albarkatun duniyar wata, tare da tabbatar da cewa suna da ingancin da za a iya dogaro da su. Wannan zai zama ta harbi tsuntsu biyu da dutse guda, na farko zai saukaka sufurin jigila da kuma kula da gyaran tashar yadda ya kamata.
Babban jagoran tsara aikin binciken duniyar watan, Wu Weiren ya ce kasar Sin ita ce ta farko a duniya da ta kera injin buga tubali ko bulon gini na kasar duniyar wata ta hanyar amfani da kayan aiki da aka sarrafa daga albarkatun duniyar watan. Injin yana aiki ne ta hanyar janyo makamashin hasken rana tare da kaiwa tarin kasar buga tubalin. Daga nan kasar za ta narke idan zafin makamashin ya kai digiri 1,400 zuwa 1,500 a ma’aunin Celsius, inda hakan zai bayar da damar buga bullon cikin sauki a duk yanayin girman da ake bukata.
Tuni dai aka aike da wani samfurin tubalin kasar duniyar wata da aka sarrafa da wasu kayayyaki makamantan na duniyar wata domin nazari a kai a tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin don gano irin sinadaran dake ciki da kuma karkon tubalin. Ana sa ran dawo da samfurin tubalin zuwa doron kasa a karshen 2025.
Fatan kasar Sin kamar yadda shugaban tsara wannan aiki Mista Wu ya bayyana shi ne, sauran kasashen duniya su shiga cikin wannan bincike a dama da su wajen samun nasarar gina katafariyar tashar binciken albarkatun duniyar wata ta kasa da kasa, saboda a kullum burin Sin shi ne gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp