Kasar Sin ta sanya kudurin zamanantarwa gaba don inganta daukacin sassan tattalin arziki har ma da zamantakewar al’umma a kasar domin tafiya da zamani. Sabon salon da ake gani na zamanantar da bangaren jigilar kayayyaki a kasar Sin ya kara nuna ci gaban da kasar ke samu, ba kawai a matsayin cibiyar sarrafa kayayyaki ta duniya ba har ma da zama kashin bayan sauya fasalin harkokin jigila a duniya. A shekarar 2024, masana’antar aikewa da sakonni ta kasar Sin ta yi jigilar kunshin sakonni fiye da biliyan 175 inda ci gaban da aka samu a bisa mizanin shekara-shekara ya karu da kaso 21.5.
Amfani da fasahohin zamani kamar irin su kirkirarriyar basira ta AI, da karfin fasahar sadarwa ta 5G, da jirage marasa matuka da mutum-mutumin inji ya kawo sabon salo ga yadda ake tafiyar da harkokin jigila bisa inganci. Cibiyoyin ajiye sakonnin da ake jigila na shaida sabon sauyi don su dace da abin da ake bukata a zamani. Yanzu haka katafariyar ma’ajiyar manyan kayayyakin jigila ta zamani da aka fara samarwa a kasar Sin a gundumar Jimo ta birnin tashar tekun Qingdao da ke gabashin kasar ta shiga aiki gadan-gadan.
- Shugabannin Sin Da Kongo (Brazaville) Sun Aike Da Wasikun Taya Murna Ga Taron Ministocin Kula Da Aiwatar Da Sakamakon Taron FOCAC
- Gwamnatin Tarayya Ta Soke Faretin Ranar Dimokuraɗiyya, Tinubu Zai Yi Wa ‘Yan Ƙasa Jawabi
Na’urori na gudanar da komai bisa amfani da karfin fasahar sadarwa ta 5G a ma’ajiyar inda hakan ya bayar da damar tafiyar da hada-hadar kunshin manyan sakonni a kalla 24,000 a kullum. Ana aiki da motoci masu sarrafa kansu a farfajiyar ma’ajiyar tare da kula da kai komonsu ta amfani da kirkirarriyar basira don magance cin karo da juna. Wadannan fasahohi da aka yi amfani da su sun taimaka wajen magance tsaikon ayyukan jigila ko jirkita sakonni da sauran abubuwan da ajizancin dan’adam zai iya haifarwa.
Kazalika, amfani da na’urori masu sarrafa kansu a manyan tashoshin jigilar kwantenoni ta teku da ke Tianjin, da Guangzhou da kuma tashar teku mai zurfi ta Yangshan dake Shanghai na ci gaba da kyautata ayyukan jigila zuwa ketare. Sabuwar fasahar da aka samar ta tashar tekun zamani mai amfani da karfin fasahar 5G+ da kirkirarriyar basira a Tianjin, da sabon sashe na hudu na tasahar Nansha ta Guangzhou, duka sun kara sauri da saukaka ayyukan sauke kaya da lodi da tsara adana su cikin sauki. Tashar Yangshan kuwa wacce ke da sashen hada-hadar kayayyaki mai amfani da na’urori mafi girma a duniya da ake samun shige da ficen kwantenoni fiye da miliyan 6 da dubu 300 duk shekara, ta zama gagarabadau ta fuskar hutar da dan’adam wajen gudanar da ayyuka a sassa masu hatsari ga rayukansa.
Zamanantar da ayyukan jigila a kasar Sin ba ta tsaya kawai a manyan birane ba, hatta kauyuka su ma suna shaida wannan sabon sauyi. Misali, a kauyen Longjing na yankin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, ana amfani da jirage marasa matuka wajen sufurin kayayyakin amfanin gona masu manyan daraja kamar su danyen ganyen shayi zuwa manyan ma’ajiyoyi. Sufurin dake daukar tsawon mintuna 45 zuwa 60 a halin yanzu ana yi cikin mintuna 10 kacal.
A Shenzhen dake kudancin Sin ma, ana amfani da jiragen marasa matuka wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya ta yadda hakan ke magance tsaikon da ake samu saboda cunkoson motoci a tituna da kuma taimakawa wajen ceto rayukan marasa lafiya da ke bukatar daukin gaggawa. Bugu da kari, an samar da tsarin sufurin jirage masu tafiya kusa da doron kasa a lardunan Jiangxi, Sichuan da Guangxi inda ake fuskantar dimbin kalubalen fadada hanyoyi saboda yanayin tsaunukansu.
Tabbas, duka wadannan sun zo da wani irin sabon salo a duniya da kasashe za su yi koyi da kasar Sin wajen zamanantar da sha’anin jigilarsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp