ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zan Ci Gaba Da Ɓata Wa Masu Sukar Tinubu Rai Da Ayyuka – Wike

by Sadiq
1 year ago
Tinubu

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce zai ci gaba da ɓata wa masu ƙin Shugaba Bola Tinubu rai ta hanyar aiwatar da ƙarin manyan ayyuka na ci gaba.

Wike ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da sabbin tituna a unguwar Katampe da ke Abuja.

  • Yadda Kasar Sin Ta Zo Da Sabon Salon Zamanantar Da Sashen Jigilar Kayayyaki
  • An Gudanar Da Taron Ministoci Masu Daidaita Ayyukan Da Aka Amince Yayin Taron FOCAC

Titunan sun haɗa da Arterial Road N16 (Shehu Shagari Way) daga Ring Road 1 (Nnamdi Azikiwe Way) zuwa Arterial Road N20 (Wole Soyinka Way).

ADVERTISEMENT

Shugaba Tinubu da kansa ne ya halarci bikin ƙaddamarwar a ranar Laraba.

A cewar Wike, akwai mutane da ke jin haushi da ci gaban da Tinubu ya kawo tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

LABARAI MASU NASABA

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ya ce ya fahimci haka ne bayan kallon wani shiri a talabijin inda ya ga wasu mutane na nuna rashin jin daɗi.

Wike ya ce wannan baƙin ciki na su shi ne ke ba shi ƙwarin gwiwa.

“Na ji wani irin abu a zuciyata, sai na kunna talabijin. A nan ne na gano cewa wasu na cikin baƙin ciki saboda abubuwan alheri da ake yi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Yanzu da na gane suna cikin baƙin ciki, zan ci gaba da sanya musu ƙarin ciwon zuciya. Farin cikinmu na ƙaruwa ne da jin haushinsu. Wannan shi ne sabon aikina na ci gaba da sa musu hawan jini.”

Wike ya yi raha da cewa yayin da suke cikin fushi da damuwa, shi da shugaban ƙasa za su ci gaba da dariya da gudanar da ayyuka.

Ya gode wa Shugaba Tinubu bisa jagorantar abin da ya kira “juyin juya hali na ci gaba.”

MASU ALAKA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Next Post
Gobara Ta Ƙone Wani Gidan Mai A Legas

Gobara Ta Ƙone Wani Gidan Mai A Legas

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.