Kungiyoyin ma’aikatan jami’a na SSANU da NASU sun gudanar da zanga-zangar lumana a harabar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, jihar Kaduna.
Zanga-zangar dai wani ɓangare ne na yajin aiki da suke gudanarwa kan albashinsu da suka ce gwamnati tarayya ta rike musu na tsawon watanni huɗu a shekarar 2022.
- Shin Da Gaske Tashe A Kasar Hausa Na Shirin Tashi?
- Gwamna Zulum Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan 1 Domin Horas da Malaman Firamare A Borno
Wakilinmu ya tabbatar da cewa, baya ga zanga-zangar da ma’aikatan suka gudanar a ranar Talata, ma’aikatan sun toshe wasu muhimman kofofin shiga jami’ar da ke Samaru.
Mohammed Yunusa shine shugaban shiyar yayin da yake bayani ga kafafen yada labarai, ya roƙi gwamnati da ta yi gaggawar biyansu albashinsu da sauran buƙatunsu domin gujewa durkushewar ci gaban jami’o’i a kasar baki daya.
“A watan Fabrairu an biya takwarorinmu na ASUU na su bashin amma mu an yi biris da mu”
Dukkan kungiyoyinmu sun yi zanga-zanga kan haka, mun kuma rubuta wasika ga gwamnati domin samun daidaito amma shiru kake ji ya zuwa yanzu.
Yanzu haka, komai ya tsaya cak a cikin jami’ar ba ruwa ba wuta ba karatu dakunan karatun duk a kulle suke.