Gulikiz Igarbeydi mai horas da wasan kwallon kafa ce a jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin. Yayin da take matashiya ’yar makaranta, ta kan tambayi kan ta cewa, yaushe ne ’yan mata za su samu damar buga kwallon kafa kamar takwarori su maza a Xinjiang?
Lokacin da take karatu a kwaleji, Gulikiz ta yi kokarin samun ’yan uwan ta ’yan mata masu sha’awar buga kwallo, amma hakan na da wuya, don haka ta kan jira ne kawai idan yara maza sun dakata sannan ta dan buga kwallo.
A yanzu Gulikiz na da shekaru 46 da haihuwa, kuma ko shakka babu abubuwa sun sauya sosai. Gulikiz ta riga ta zama kocin kwallon kafa ajin ’yan mata, a wata makarantar midil dake garin Bageqi a gundumar Hetian. Tana horas da tawagar ’yan mata 27, kuma akwai karin wasu dake sonsu ma su shiga kungiyar da take horaswa.
- Sin Na Taka Rawar Gani Wajen Raba Fasahohinta Na Bunkasa Tattalin Arziki Na Zamani Da Sauran Kasashe Masu Tasowa
- Gwamnati Ta Dakatar Da Daraktocin Hukumar Sufurin Jiragen Sama 5 Sa’o’i Kadan Bayan Sauke Shugabanninsu
Game da sauyin da take gani a yanzu, Gulikiz ta ce “Lokacin da nake dalibta, iyaye na kan ce wasan kwallon kafa na maza ne, kuma malamai ma na cewa kwallon kafa na bukatar takara mai tsanani, don haka wasan bai dace da mata ba. A wannan lokaci cikin shekarun 1990 a jihar Xinjiang, akwai wannan yanayi da aka nuna bambanci tsakanin maza da mata.
A ajin da ta yi karatu, Gulikiz ta ce dalibai su 77 ne, kuma su 7 ne kacal mata. Kana in ban da ita, ba wata mace dake buga kwallon kafa.
Ta kara da cewa, “A wancan lokaci mutane na yiwa mace dake buga kwallon kafa wani irin kallo, har ma makwafta kan nuna ta da yatsa”. Amma bisa sha’awar ta ga kwallon kafa, Gulikiz ta zama mai koyar da wasannin motsa jiki a makarantar midil dake Hetian, bayan da ta kammala karatu daga makaranta, duk da hakan ba abu ne da ta cimma cikin sauki ba.
Ta ce “A da can, iyaye da dama ba su damu da ilimin yaran su ba, abu ne mai sauki yaro ya ki zuwa makaranta. Kuma ’yan mata na jin kunyar yin wasannin motsa jiki tare da takwarorinsu maza, kuma ba su cika son motsa jiki sosai ba.”
Amma a shekarun baya bayan nan, Gulikiz na ganin al’ummun Xinjiang sun samu karin damammaki na yin tafiye-tafiye zuwa wurare masu yawa. Kaza lika, ta hanyar kallon talabijin da shiga yanar gizo, suna kara fahimtar inda duniya ta sa gaba, tunaninsu ya kara fadada, wanda hakan ke sauya musu alkibla game da yadda za su yi renon yaran su ta fuskar ba su ilimi, da ma batun shigar yara mata cikin wasannin kwallon kafa.
A shekarun baya bayan nan, sha’anin kwallon kafa a Xinjiang ya samu bunkasa, bisa tallafin da lardunan kasar Sin da dama ke bayarwa. Yanzu haka larduna 19 da birane, ciki har da Beijing, da Shanghai, da Jiangsu, suna hadin gwiwar baiwa biranen dake Xinjiang tallafi a fannonin raya wasan. Tun daga shekarar 2020 zuwa yanzu, tallafin na su ya kai sama da kudin Sin yuan biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.37. Kari kan hakan, malaman makarantu sama da 14,000 sun samu horon kyautata koyar da dalibai a Xinjiang, inda da daman su suke taimakawa wajen raya sha’anin kwallon kafa a jihar.
Gulikiz ta ce “Ina jin dai mafarki na ya zama gaskiya cikin ‘yan shekaru kadan.”
Da take bayyana yanayin da ake ciki, shugabar makarantar midil ta garin Bageqi Bai Huilin, ta ce “Kusan dukkanin makarantu dake gundumar Hetian dake kudancin jihar Xinjiang sun riga sun kafa kungiyoyin kwallon kafa na mata. Kuma adadin ’yan mata dake shiga wasan na kwallon kafa ya kai kaso kusan 20 bisa dari, bisa jimillar ’yan matan makarantun.”
Alkaluma sun nuna cewa, makarantu 799 sun shiga gasar lashe kofin kwallon kafa ta mata mai lakabin “Hemei Cup”, gasar da gundumar Hetian ta shirya a farkon watanni shida na shekarar nan ta 2023. Kaza lika a gundumar Kizilsu Kirgiz, an gudanar da gasanni sama da 20 cikin shekarar nan ta bana, gasannin da suka samu halartar ’yan makaranta kusan 13,000 daga firamare, da midil, ciki har da ’yan mata da adadin su ya kai rabin jimillar ’yan wasan. Ga wadannan yara mata, karfin gwiwar su shi ne babban jarin su, wanda kuma suke samu daga taka leda yadda ya kamata.
Munire Adili, daliba ce dake aji na 5 a makarantar firamare dake garin Gujiangbage na birnin Hetian, ta kuma ce “Yayin da mahaifiyata ta ga shaidar nasarar da na samu a gasar kwallon kafa, ta yi matukar farin ciki, har ta nunawa makwaftan mu wannan takardar shaida.”
Kusan rabin shekarar nan, Munire ta rika sha’awar wasan kwallon kafa a duk lokacin da take kallo mata suna taka leda a makaranta. Da taimakon mahaifiyarta, ta shiga gwaji, tare da yin nasara mai yawa kafin ta samu zama mai tsaron gida, a kungiyar kwallon kafar su. Ga matashiya Munire, lashe wasanni na kara mata kwarin gwiwar haye wahalhalun rauni da take samu yayin da take atisaye.
A cewar ta “Idan kwallo ta daki mutum a fuska ko a jikinta, ana jin ciwo sosai, amma kocinmu tana karfafa mana gwiwa da cewa, kwallo ba ta da baki balle ta yi cizo. Ina fatan ci gaba da yin atisaye sosai domin samun damar wakiltar makarantar mu a gasanni daban daban a nan gaba, ta yadda zan samu zarafin ganin sauran sassan duniya.”
Ita ma daliba Bumairemu Ali, wadda ke aji na 9 a makarantar midil dake garin Bageqi, ta samu damar ziyartar wurare daban daban a jihar Xinjiang sanadiyyar kwallon kafa.
Ta kuma ce “Na yi wasu kawaye daga sassan kabilu daban daban ta hanyar buga wasan kwallo a wurare masu yawa. Mu kan yi musayar fahimta ta yanar gizo, game da kwallo da harkokin karatu.”
Makarantar garin Bageqi, na amfani da kudaden da take samu wajen taimakawa daliban ta ’ya’yan makiyaya da dukkanin abubuwan da suke bukata na buga wasa, kama daga takalma, da sufuri, da matsuguni, ta yadda za su samu damar shiga a dama da su a gasannin da ake shiryawa.
Yanzu haka, Bumairemu ta kusa kammala karatun midil, tana kuma da kyakkyawan fata game da makomar rayuwarta. Game da hakan, ta ce “Ina da zabi mai yawa a nan gaba, amma kwallon kafa na kan gaba cikin abubuwan da zan baiwa muhimmanci.”
A duk lokacin da koci Gulikiz ta sanya matasan dalibai mata da take horaswa a gaba suna taka leda, ta kan samu kwanciyar hankali. Ta tabbatar cewa, a yanzu lokaci ya wuce da iyayen yara mata za su rika kiran su domin su tafi aikin gona, a lokacin da ya kamata a ce suna aji, ko kuma a rika tsokanar su saboda kawai suna buga kwallon kafa.
Kungiyar wasan kwallon kafan mata ta kasar Sin ta taba kasancewa a kan gaba a duniya, amma a shekarun baya baya nan, sakamakon kungiyar na rashin samun nasarori a wasan, ya sa karfin kungiyar bai kai matsayin na gaba a duniya ba, dalilin da ya sa hakan shi ne rashin samun matasa da yara mata masu yawa da suka kware a wasan.
A wadannan shekaru, an kara maida hankali ga wasan kwallon kafa, kasar Sin ta kara nuna goyon baya ga wasan kwallon kafa, inda aka kyautata tsarin raya wasan a makarantun kasar, wannan mataki ya taimaka wajen raya sha’anin wasan kwallon kafa na kasar Sin. A matsayin tushen raya wasan kwallon kafa mata da ma muhimmin bangare na raya wannan sha’ani, aikin raya wasan kwallon kafa mata a makarantu midil da firamare na kasar Sin ya kara jawo hankalin zamantakewar al’ummar kasar.
Tun daga shekarar 2009, gwamnatin jihar Xinjiang ta fara gudanar da ayyukan raya wasan kwallon kafa a makarantun jihar. Jihar Xinjiang tana da fadi, da kabilu da dama, kana jihar Xinjiang jiha ce dake da ’yan kabilar Uygur. Daliban makaranta za su ji dadin wasan da kyautata rayuwarsu ta hanyar buga wasan kwallon kafa. A matsayin wasan dake bukatar mutane da dama, wasan kwallon kafa zai taimakawa dalibai yin hadin gwiwa da juna, da sauike nauyin dake wuyansu, da yin hakuri da sauransu.
Yawancin daliban da ke shiga tawagar mata ta kungiyar kwallon kafa ta matasa ta jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, daliban kananan kabilu ne, kuma iyali da addini suna shafar wadannan dalibai shiga harkar kwallon kafa. Don haka shiga wasan kwallon kafa zai taimakawa dalibai mata su kara shiga tsarin zamantakewar al’umma da jin dadin zaman rayuwa na zamani. (Zainab Zhang)