Kamar yadda Bahaushe kan ce “Lafiya Uwar Jiki”, babu mai fushi da ke, mun sani cewa daya daga muhimman fannonin kare lafiyar dan adam shi ne fannin lafiyar ido. Ga wadanda suke fuskantar larurar gani ko ciwon ido, su kan shiga wani yanayi mawuyaci, tare da fafutukar neman magani.
To sai dai a kasar Ghana dake yammacin nahiyar Afirka, masu irin wannan larura sun yi gam-da-katar, domin kuwa, tun daga watan Nuwambar bara, wata tawagar likitocin kasar Sin da aka aike kasar, tana gudanar da tiyata kyauta, ga masu fama da matsalolin ido, ciki har da masu fama da cutar yanar ido ko “cataracts” a Turance.
Al’ummun kasar Ghana da dama, sun ci gajiya daga hidimomin kula da idanu da tawagar likitocin na kasar Sin ke bayarwa. Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu. Jama’a na samun damar a duba idanunsu, tare da ba su magani, ko ma yi musu aiki idan ta kama, a cibiyar da likitocin na Sin ke aiki, wadda take asabitin ido na LEKMA, a birin Accra, fadar mulkin kasar.
Ga masu karamin karfi dake fama da yanar ido, abu ne mai wahala su iya samun magani, duba da cewa, aikin wannan cuta na da tsada, don haka wasu daga cikinsu, su kan hakura da yanayin da suke ciki, har ta kai ga sun rasa ganin su baki daya. Amma zuwan wannan tawaga ta likitocin ido daga kasar Sin, ya farfado da fatansu na samun lafiya, matakin da ke matukar samun yabo daga dukkanin al’ummar kasar baki daya.
Idan za mu iya tunawa, tun a baya, mahukuntan kasar Sin sun sha alkawarta tallafawa kasashe masu tasowa ta fannin kiwon lafiya, kuma karkashin manufofin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, Sin ta aiwatar da matakai daban daban, na agazawa kasashen Afirka da kayan aiki, da tallafin kwararru, wanda tuni kasashen nahiyar da dama suka ci gajiyar hakan. La’akari da haka, ma iya cewa, Sin tana cika alkawura da ta dauka ga kawayenta na Afirka, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu, game yaukakar alakar Sin da abokanta na nahiyar Afirka, da ma burin kasar ta Sin, na samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya daga dukkanin fannoni. (Saminu Hassan)