A cikin shekara daya da ta wuce, kwararrun likitoci 1,616 da suka samu horo a Nijeriya sun koma kasar Birtaniya da aiki.
Hakan na kunshe ne acikin wani sabon bincike da Majalisar Likitoci (GMC) ta kasar Birtaniya ta fitar.
- Abin Da Ya Haddasa Gobara A Gidan Rediyo Nijeriya Kaduna – ‘Yan Kwana-kwana
- Yadda Na Hana ‘Yan Boko Haram Mayar Da Jihar Neja Hedikwatarsu – Tsohon Gwamnan Jihar
Nijeriya ita ce kasa ta uku a jerin kasashe masu bayar da gudummawa a bangaren likitanci ga ma’aikatar lafiya ta Birtaniya wadanda ba ‘yan kasar Birtaniya ba ne, bayan Indiya da Pakistan da ke da likitoci 2,402 da 2,372.
Rahoton ya bayyana cewa, a shekarar 2014, likitocin Nijeriya 181 ne kawai suka koma kasar Birtaniya a shekarar 2014, wanda hakan ya sa Nijeriya ta zama ta 11; zuwa shekarar 2022, adadin likitocin ya karu zuwa 1,616, wanda hakan ya sa suka zama na uku a jerin kasashen da ke bada gudunmawa a fannin likitanci a kasar Birtaniya.