Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya (MDD), sun bi sahun takwarorinsu na duniya wajen yin shiru na minti daya domin tunawa da ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya da suka rasa rayukansu a yakin da Isra’ila da Hamas ke ci gaba da yi a Gaza.
Da yake jawabi, mukaddashin babban jami’in MDD a Nijeriya, babban wakilin sashen ci gaban kasashe na UNDP, Mohammed Yahya, ya bayyana cewa, “cikin alhini muke bin sahun dukkan ma’aikatan MDD a fadin duniya wajen yin shiru na minti daya a yau Litinin 13 ga Nuwambar 2023 domin karrama abokan aikinmu da aka kashe a Gaza”.
Ya bayyana haka ne a wani takaitaccen taron da aka yi tare da sassauta tutar Majalisar a babban ofishinta da ke Abuja
“Kamar yadda kuke gani, an sassauta tutar Majalisar Dinkin Duniya zuwa rabin turke a matsayin alamar girmamawa a wannan taro. “Ina neman dukkanmu mu yi shiru na tsawon minti daya yayin da muke girmama abokan aikinmu da suka mutu,” in ji shi.
Bugu da kari, ya bukaci dukkan ma’aikatan su nuna alhininsu ga marigayan, yana mai jaddada muhimmancin girmamawa da kuma tunawa da wadanda suka sadaukar da kansu wajen yi wa al’umma ayyukan jin kai hidima.
Domin cika umarnin da aka bayar, har ila yau an yi shiru na minti daya a tsakanin ma’aikata 86 da ke halartar taron koli na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya da ke gudana a Jihar Neja. Daidai misalin karfe 1:30 na rana, mahalarta taron sun mike tsaye don yin shiru na minti daya domin girmama abokan aikinsu da suka mutu a Gaza.
Bayan shirun na minti dayan ne, Yahaya ya kammala sakon nasa da kyakkyawar ta’aziyya da addu’a, yana mai cewar, “Allah ya sa sun huta.”