Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Ngali da ke yankin Logara a karamar hukumar Ngor Okpala ta Jihar Imo, inda suka harbe wani shugaban al’umma a ranar Laraba.
LEADERSHIP ta tattaro cewa shugaban al’ummar garin, Cif Monday Eke yana jawabi ga ‘yan uwansa a kauyen, ‘yan bindigar sun zo ne a cikin wata jar mota kirar Camry, suka harbe shi har lahira.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce shugaban da aka kashe Monday, direban mota tifa ne ga wani Anummoo daga Umuohiagu.
A cewarsa, jar motar da aka kwace da bindiga daga hannun wani Mista Obum da ya zo jana’izar mahaifiyarsa, tuni ‘yan bindigar suka yi watsi da ita.
Majiyar ta ce, ‘yan bindigar na dauke da muggan makamai kuma sun rufe fuskokinsu lokacin da suka kai harin.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne aka kashe ‘yan sanda biyar da wasu ma’aurata a mahadar Okpala, yayin da wata guda da ya gabata ‘yan bindiga suka kashe jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence guda uku a kasuwar Eke Isu da ke unguwar Obiangwu, dukkansu a karamar hukumar Ngor Okpala a Jihar Imo.