Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Uwargida Sarautar Mata. A yau shafin na mu zai yi bayani ne akan gyaran matar da ta haihu musamman ma haihuwar fari.
Musamman haihuwar fari yawanci mata suna samun kari da yawa suna tsoron dinki idan har ki kayi sakaci jikin ki bai koma dai dai ba kin cuci kanki kullum namiji so yake ya jiki dai-dai, zama zama in kuwa ya samu bambanci ko yaya zaku rasa kan mijinsu tunda suka haihi to yawanci wannan matsalar ce.
- Za Mu Ci Gaba Da Goya Wa PCACC Baya Wajen Yaƙar Cin Hanci Da Rashawa – Gwamnatin Kano
- Yara Miliyan 1 Ke Mutuwa Duk Shekara A Farkon Watansu Na Haihuwa A Nijeriya – UNICEF
Cututtukan da su ke damun al’aurar Mata kamar yadda bincike ya nuna cewa, akwai cututtuka da yawa masu damun al’aurar ‘ya’ya mata, kama daga balagarsu zuwa fara zaukar ciki har zuwa daina al’adarsu, kamar:- Warin gaba,Warin gaba na ‘ya’ya mata ya na samuwa saboda wasu dalilai da su ke jawo shi kamar haka:
1- Tafiya ba wando. 2. Kin wanke farji bayan jima’i. 3- Kin wanke farji da ruwan dumi; misali bayan an yi al’ada. 4- Barin wando ya kai kwana uku a jiki. 5- Kama ruwa da ruwa mai sanyi karara. 6- Kin wanke gaba bayan an tsuguna a masai. 7- Mace ta ringa biya wa kanta bukata da hannu ko wani abu.
Wuraren da warin gaba ke fitowa uku ne;
1 Hammata, farji da kuma baki. Saboda haka lallai ne ki bada kulawa ta musamman a wannan guraren naki, don gudun samun matsala. (2) Kumburin Gaba da kaikayin gaba: Wannan cututtuka su ma su na damun al’aurar ‘ya’ya mata kwarai da gaske. (3) Zafin gaba. (4) Zubar Ruwa. (5) Rashin Haihuwa. (6) Sanyi ko zafin Mahaifa.
Wadannan su ma su na hana mace ta samu ciki saboda illolin da ke tattare da hakan. Karin Bayani: Akwai cututtuka da yawa da su ke samun al’aurar mata, saboda ba ta rabuwa da danshi wanda ta nan ne wasu kwayoyin halitta su ke samun zama a cikin al’aurar tasu.
A na kiran su Micro–organism da Turanci. Ku sani cewa shi farji da a ke magana a kan cututtukansa shi ne wanda Allah ya halitta da wani sinadari na mayen karfe da wata tsoka kuma tana da baki guda biyu hagu da dama. Yayin da sha’awar mace ta motsa sai ta rika motsi dai-dai kuma tana iya yin rauni har ta daina motsi.
Wannan tsoka kamar fulogi ne a jikin mace, yayin da ta yi ma ta yawa, sai ta kasa motsi, daga nan sai sha’awar ‘ya mace ta dauke, domin ita wannan tsoka ita ce ke feso wani ruwa wanda shi ke sauko da wani ruwa da ya ke da jin dadin mu’amalar jima’i kuma yake sa wani zaki tsakanin mace da miji.
Idan daya daga ma’aurata ya samu matsala, sai ka ga auren ya ki zaman lafiya. Amma idan babu matsala sai ka ga a na zaune lafiya cikin shauki da annashuwa.
Mafi yawa mata masu ciki su na kamuwa da cututtuka daga wasu kwayoyin halitta da ke rike al’aurar mata, saboda gabansu ba ya rabuwa da danshi. Wadannan kwayoyin halittu su ne, bacteria, fungi da sauransu.
Alamomi masu nuni izuwa kamuwar cutar al’aurar mace ya danganta da irin ciwon da abin da ya jawo shi.
Za Mu Ci Gaba Mako Mai Zuwa Idan Allah Ya Kai Mu