Akalla mutum takwas da ake zargin suna da alaka da sayar naman matattun shanu kwamandan hukumar tsaron Cibil Deffence ta Nijeriya reshen Jihar Gombe, Muhammad Bello, ya gurfanar bisa laifin sayar da naman matattun shanu ga mutane.
Bello ya ce tawarar ta mutum takwas ta hada da wata mata mai suna Mary Paul daga Jihar Delta da kuma wasu maza bakwai da suka kware wajen saye da sayarwa gami da gasawa ga kwastomomi.
- Shawarar Kasar Sin Ta Gina Al’ummar Duniya Mai Mokamar Bai Daya
- Tsantseni Da Gudun Duniya Na Annabi S.A.W (2)
Wakilinmu ya samu labarin cewa Paul tana gasa mushen naman tare da naman daji kafin ta kai kasuwa, inda jama’a ke sayan naman a hannun ‘ya’yanta.
Da yake magana ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saad Buhari, kwamandan ya bayyana cewa kungiyar tana gudanar da wannan sana’ar ne a cikin shekaru biyu da suka gabata, inda ya kara da cewa wadanda ake zargin sun gudanar da sana’arsu ne duk da rashin lafiyar da abin yake haifarwa.
Ya ce, “Sun kware wajen sayar da mushen naman, musamman na saniya. Sun shafe shekaru biyu suna yin haka kafin a yi nasarar cafke su ta hanyar samun bayanan sirri.
Matar mai shekaru 40 ta ce an sanar da ita ta zo ta sayi wata saniya da ta fada rijiya kafin jami’an hukumar su kama ta.
Mahaifiyar ‘ya’ya hudu ta ce, “Ni ’yar Jihar Delta ce; Na yi shekara biyu a Gombe. Aka ce min wata saniya ta fada cikin rijiya ta mutu, sai muka je domin mu sayo. Na yi kokari na sarrafa ta tare da gasawa hade da wani naman daji.