Ofishin Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwaiar Tarayyar Turai da sauran takwarorinsu sun kamala wani shirin yaki da cin zarafin mata a Nijeriya mai lakabin ‘spotlight initiatibe’ tare da mika ragamar cibiyoyin gudanar da aikin ga gwamnatin Nijeriya.
An kamala shirin ne a otel na Transcorp da ke Abuja a tsakiyar makon nan inda wasu ministoci da shugabannin hukumomin gwamnati suka halarta.
- Majalisa Na Fuskantar Kalubalen Amincewa Da Kasafin Naira Tiriliyan 27.5 Na 2024
- Kamfanonin Siminti Ke Haifar Da Kashi 7 Na Dumamar Yanayi A Duniya – Dangote
A jawaban da suka gudanar daban-daban, Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Mattias Schmale da Wakiliyar Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS, Samuela Isopi sun ce shirin ya samu nasara bisa yadda yake bai wa matan da aka ci zarafi damar zuwa cibiyoyin kulawa don sake farfado da rayuwarsu, kana suka ce mika shirin daga gwamnati ne zuwa gwamnati kasancewar su goyon baya suka bayar amma gwamnati ce ta aiwatar da shirin.
Da yake jawabi, Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu wanda Dr. Lare Akanye ya wakilta, ya bayyana cewa, “An samu ci gaba a yaki da cin zarafin mata tun daga lokacin da aka kaddamar a 2018. Akwai cibiyoyi daban-daban da aka samar a wasu sassa na kasa domin gudanar da aikace-aikacen da suka shafi ceto rayukan wadanda aka ci zarafinsu da kuma sake farfado da rayuwarsu
“Gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa wurin bayar da goyon baya ga dukkan ire-iren wadannan shirye-shirye na ci gaban rayuwar ‘yan kasa. Kuma ya yaba wa Tarayyar Turai da ta bayar da kashi 5 cikin 100 na taimakon kudin da ta ware a duniya inda Nijeriya take cin gajiyar wajen miliyan 500.” In ji shi
Hakazalika, Ministan Shari’a, Fagbemi Lateef ya bayyana cewa, ya yi magana da kungiyar gwamnoni domin fadada tsare-tsare da shirye-shiryen da tarayya ke gabatarwa game da yaki da cin zarafin mata.
Yanzu haka, a cewarsa, ma’aikatarsa ta mike haikan wurin ganin ana hukunta duk wadanda aka kama suna cin zarafin mata, “yanzu haka akwai shirin da muka yi na tabbatar da cewa ana hukunta masu cin zarafin mata a makarantu. Za mu tabbatar da kare ‘yancin wadanda al’amarin ya rutsa da su da kuma tabbatar da cewa wadanda suka aikata sun gurfana a gaban kuliya.
“Muna jin dadin cewa a yau da ake rufe wannan shiri na yaki da cin zarafin mata na ‘Spotlight Initiatib’e, an samu ci gaba a kan manufar shirin kuma Wannan ya kara nuna cewa idan muka yi kawance da abokan ci gaba, za mu samar da sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’umma.”
Shi ma a jawabinsa, Sarkin Shonga, Dr. Haliru Yahaya Ndanusa, ya bukaci al’umma su hada karfi da karfe wajen kawar da dukkan wani nau’i na cin zarafin mata domin kyautata rayuwarsu.
Ya ba da misalin cewa matukar aka bari cin zarafin mata ya ci gaba da gudana to babu shakka za a zare musu walwala a rayuwarsu inda hakan kuma zai shafi hatta ci gaban kasa saboda mata masu ilimi da ke cikin kwanciyar hankali suna ba da gudunmawa ga ciyar da kasa gaba.
Shi kuwa Babban Sufeton ‘Yansandan Nijeriya, Kayode Egbetokun wanda DIG Amina ta wakilta, ya nunar da cewa, ‘Yansanda ne ke jagorantar yaki da duk wani nau’i na cin zarafin mata kuma za su ci gaba da tabbatar da fatattakar duk wadanda suka dauki cin zarafin mata dabi’a.
Har ila yau, ya ce rundunar ta samar da sashe na musamman a kan kare hakkin mata a daukacin jihohi 36 har da Abuja. Kuma za su ci gaba da kai daukin gaggawa duk lokacin da aka kira su domin kai agaji ga matan da aka ci zarafinsu.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin sun yi bayanin yadda rayuwarsu ta kasance a baya da kuma a yanzu, kana masu wasan kwaikwayo suka nishadantar da fadakar da mutane game da muhimmancin taimaka wa matan da aka ci zarafinsu.