A ranar Littinin ne Majalisar dokoki ta jihar Nasarawa ta dakatar da tantance Hon. Yakubu Kwanta, tsohon Kwamishinan Muhalli, saboda gazawar da ya yi na bayyana a gaban kwamitin Majalisar kan Muhalli don kare ayyukan kasafin kudin Ma’aikatar a shekarar 2024, wanda ya jagoranta a lokacin da yake Kwamishina.
‘Yan Majalisan sun bayyana kin bayyana a gaban kwamitin majalisan a lokacin da ta bukace shi a matsayin rashin biyayya ga majalisar da ta tantanceshi a lokacin da sunanshi ya bayyana cikin kwamishinoni a shekarar 2024.
- Yawan Tikitin Kallon Fim Din “Ne Zha 2” Da Aka Sayar a Karshen Mako Ya Shiga Sahun Gaba Na Fina-Finai 5 A Arewacin Amurka
- Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Tarayya Daga Riƙe Wa Ƙananun Hukumomin Kano 44 Kuɗaɗensu
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Rt. Hon. Danladi Jatau ne ya dakatar da tantance Hon. Yakubu Kwanta wanda sunansa ya kara bayyana cikin jerin kwamishinoni a wannan shekarar.
Kakakin Majalisan ya amince da kudirin dan majalisa mai wakiltar mazabar Keana kuma shugaban Kwamitin Majalisar kan Muhalli, Hon. Muhammed Adamu Omadefu, wanda ya bukaci dakatarwar a yayin tantance kwamishinan a zauren Majalisar da ke Lafiya, babban birnin jihar.
Hon. Jatau ya ce, Majalisar za ta sake duba batun tantance shi ne kawai idan ya aika da wasikar neman uzuri mai karfi ga Majalisar kan aikata laifi da rashin biyayya da ya yi lokacin da yake Kwamishina.
Ya ce, Majalisar ba za ta bari wani jami’in gwamnati ya zubar da darajar Majalisar ba.