Masu lalurar makanta 44 ne suka zana jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta shekarar 2024 a ranar Litinin a cibiyar musamman da aka ware domin jarrabawar ga makafi a Bauchi da ya gudana a cikin jami’ar ATBU da ke Yelwa.
Dalibai makafi 44 sun fito ne daga jihohi hudu na arewa maso gabas da suka kunshi Bauchi, Gombe, Yobe da Borno.
- Yanzu-Yanzu: Jami’an Tsaro Sun Cafke Jami’in Binance A Kenya
- Uba Da Ɗa Sun Mutu Wajen Ciro Waya A Masai A Kano
JAMB a karkashin shirinta na musamman na bai wa masu bukata ta musamman cikakken dama irin ta kowa domin cimma burukansu na rayuwa ne aka zana jarabawar wacce ake yi a cibiyoyi sama da goma a fadin Nijeriya.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida kan jarabawar, Ko’odinetan jarabawar makafi a Bauchi, Farfesa Salisu Shehu, ya bukaci gwamnatin jihar Bauchi da sauran jihohin da suke arewa maso gabas da su dukufa wajen wayar da kan mutanen da ke fama da lalura ta musamman domin ganin sun samu cin gajiyar shirye-shiryen da JAMB ke yi musu.
A cewarsa, muddin aka wayar da kan masu bukata ta musamman tare da iyayensu tabbas za a samu karin masu shigowa a dama da su wajen zana jarabawar JAMB domin kyautata musu rayuwarsu ta gobe.
Ya nuna gamsuwarsa kan yadda daliban suka nuna da’a a yayin jarabawar, ya ce, an shirya musu komai tun daga zuwansu daga jihohinsu da masaukinsu da abinci da zirga-zirgansu hadi da kudin motan zuwa da komawa dukka kyauta ne.
Shi ma a jawabinsa, kwamishinan yada labarai na jihar Bauchi, Kwamared Usman Dan Turaki, ya nuna farin cikinsa kan kyakkyawar tsarin da JAMB ta yi wajen shigo da masu bukata ta musamman cikin tsarin jarabawar sharar fagen shiga manyan makarantu.
Ya ce, tabbas wannan shirin abun yaba ne domin kowa zai samu damar cimma burinsa, ya na mai cewa ta hanyar masu ta musamman ana iya samun gagarumin cigaba a kasa baki daya.
Ya gode wa gwamnatin tarayya a karkashin Bola Ahmed Tinubu kan yadda take tunawa da kowa a cikin shirye-shiryenta.
Kazalika, ya ce daga cikin muhimman abubuwa da gwamnatin jihar Bauchi a bisa jagoranci Bala Muhammad ta sanya a gaba har da kyautata rayuwar masu bukata ta musamman da kuma sanya su a gaba-gaba wajen kowace irin shirye-shiryen cin gajiyar romon demukuradiyya.
Har ila yau mamba a sashin bayar da dama ga kowa ta JAMB, Farfesa Hadiza Isah Bazza ta bukaci daliban da su jajirce wajen ganin sun cimma burukansu na rayuwa musamman a bangaren ilimi.
Ta kuma bukaci iyaye da su cigaba da mara wa ‘ya’yansu da ke fama da bukata ta musamman baya a dukkanin abubuwan da suka sanya a gaba domin su ma suke kai rayuwarsu gaba kamar yadda kowa ke samun dama.