Zhang Qiongfen yar kabilar Yi ce, wadda kafin ta fara aikin surfani, ta kan yi kananan ayyuka a wuraren gini, kamar daukar turmi, da bulo da siminti, sai dai ba ta samu kudin shiga isasshe ba, ga kuma gajiya sosai.
Amfani da aladun gado da ba na kayayyaki ba wajen kawar da talauci mataki ne da ake aiwatarwa karkashin manufar raya kauyuka da gwamnatin Sin ta dauka. Ta wannan hanya, an horas da Zhang Qiongfen kafin ta kama wannan aiki, kuma ta hakan, ba ma kawai Zhang ta samu kudin shiga mai kyau ba, har ma ta jagoranci sauran masu aikin irinta wajen yayata fasahar surfani irin ta Yi a duniya, inda ake iya ganin wannan fassaha a makon nuna kwalliya da sutura da aka gudanar a biranen Beijing, da Shanghai da Milan.
- Kasar Argentina Ta Ba Shugaban CMG Lambar Yabo
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Fahimtar Kasar SinÂ
Aladun gado da ba na kayayyaki ba, na taimakawa gundumar Chuxiong na lardin Yunnan wajen rayawa da farfado da kauyuka. A shekarar 2022, shaanin surfani irin na kabilar Yi na gundumar ya samar da karin riba har yuan miliyan 245. Sai kuma a cikin farkon watanni 9 na bana, yawan karin ribar da wannan shaani ya samar ya kai yuan miliyan 172. Kana a tsakanin shekarar 2012 zuwa ta 2022, yawan mata masu aikin surfanin a Chuxiong ya karu daga dubu 27.5 zuwa dubu 57, adadin da ya ninka sau 1, kuma yawan kudin shigar wadannan mata ya karu daga yuan 563 zuwa 3180, adadin da ya ninka sau 4.6.
Mata kamar Zhang Qiongfen, sun cin gajiyar manufar raya kauyuka, kuma yadda aka hada aladun gado da ba na kayayyaki ba, da manufar kawar da talauci, ba ma kawai ya taimakawa matan kabilar Yi wajen fita daga kangin talauci, da kyautata zaman rayuwarsu ba, har ma ya yayata fasahar surfani irin ta kabilar Yi har zuwa sassan duniya. (Mai zane da rubutu: MINA)