Jaruma a masana’antar Kannywood wadda kuma ta ke fitowa a matsayin uwa a mafi yawancin fina finanta Hadizan Saima ta koka a kan yadda matasa masu kananan shekaru wasu lokutan ke fitowa karara su na neman ta basu damar aurenta duk da cewar ita mace ce wadda ta kwana biyu a Duniya.
Hadiza ta ce babban abinda ke bata mani rayuwa a yanzu, kuma na rasa hanyar da zan bi in yi maganin abin shi ne yadda duk da yawan shekaruna a yanzu amma sai in samu yara matasa masu kananan shekaru su na tuntuba ta da maganar aure, hakan na matukar bani mamaki domin kuwa yanzu zaman aure ma yaya aka kare tsakanin manya masu hankali balantana yaro matashi da hankalinsa bai kai na manya ba ya auri dattijuwa kamar ni, inji ta.
- Kar Ku Tayar Da Hankalinku Kan Cutar Tsuntsaye – Ma’aikatar Lafiya Ta Kano
- Duniya Na Fatan Sin Da Amurka Za Su Cika Alkawuransu Cikin Hadin Gwiwa
Ni dattijuwa ce a yanzu saboda haka kamata ya yi ace na samu dattijo irina na aura ba karamin yaro wanda hankali da wayo bai gama shigarsa ba, ta kara da cewa, yanzu ta share tsawon shekaru fiye da 20 a wannan masana’antar ta Kannywood wadda ta ce ta shigo sanadiyar wata kawar ta da ita ma take jarumar fim a wancan lokacin ta nuna damuwa akan wannan abu, inda ta ce ta na koakrin gusar da abin daga tunaninta amma har yanzu ya kasa wucewa.
Jarumar na daga cikin jarumai mata da ke fitowa a matsayin iyaye a fina-finan Kannywood, inda ta samu daukaka a tsakanin shekarar 2015 zuwa yanzu duba da irin rawar da ta ke takawa a cikin shirin fim a duk lokacin da ta samu kan ta a irin wannan mata ayi na uwa,fina finanta na baya bayannan sun hada da Labarina, Manyan Mata da sauransu.