Matasan Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group reshen Jihar Sakkwato sun gabatar da Maulidin Annabi Muhammadu (SAW) na bana a bisa jagorancin jagoransu, Shehu Isma’ila Umar Almaddah Mai Diwani, a ranar Lahadin da ta gabata.
Maulidin wanda ya gudana a babban zauren taro na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ali Shinkafi da ke Sakkwato, ya samu mahalarta daga Kano, Katsina, Obajana, har ƙasar Ghana da Benin.
An gabatar da karatun Alƙur’ani mai girma da ƙasidodi na yabon Annabi (SAW) wanda Shehu Ibrahim Inyass ya rubuta.
Da yake gabatar da karatun maulidin, Shehu Isma’ila Umar Almaddah wanda ya karanta huɗubar da Shehu Ibrahim Inyass ya gabatar a wani taron maulidi da aka yi a Madinatu Kaulakha a shekarar 1960, ya bayyana cewa wurin taron maulidi, fage ne da duk halitta take taruwa waɗanda ake gani da waɗanda ba a gani saboda soyayyar Manzon Allah (SAW) ta kowa da kowa ce.
Ya ƙara da cewa, a cikin huɗubar ta Shehu Ibrahim, ya hori kowa da kowa ya sabunta imaninsa da Allah Sarki mamallakin sama da ƙasa wanda bai riƙi aboki ba, bai riƙi mata ko ɗa ba saboda Allah ya ɗaukaka ga barin waɗannan abubuwa.
Ya ƙara da cewa, “Mu riƙe Alƙur’ani da kyau, mu riƙa karantawa, idan da hali ka haddace, idan ba za ka iya yi ba; ka riƙa karantawa sosai. Alƙur’ani yana fassara kowace Hadara, yana magana da yarenta. Mu riƙe Hasidin Manzon Allah (SAW), shi ma haka yake. Cikar ma’arifa shi ne mu bi bayan Shehu Ibrahim wajen bin ƙur’ani da Hadisi.
“Sannan mu kyautata ibada don Allah, meye ma’anar haka? Ita ce mu yi ikhlasi cikin ibadunmu kamar yadda Allah ya unarce mu. Allah ya ce bai halicci mutum da aljan ba sai don su bauta mun. Imani yana ƙaruwa da ƙaruwar aiki, yana raguwa da raguwar aiki. Me zai nuna mana cewa muna aiki mai kyau? Shi ne mu ga musulmi sun kuɓuta daga sharrin harshenmu da hannayenmu.” In ji shi
Da ya juya kan batun girmama Manzon Allah (SAW), Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya bayyana cewa duk wani karatu da zai sa mutum ya ga rashin girman Manzon Allah zai zama karatu na ɓata da zai kai mutum ga halaka. Ya ba da misali da cewa malamai sun yi hani da duba Tafsirin ɗanɗawi saboda a ciki ya bayyana cewa Mala’ika Jibrilu ya fi Manzon Allah.
“Dukkan Annabawa masu girma ne, sai dai Allah ya fifita wasu a kan wasu. Kuma duka a cikinsu babu kamar Manzon Allah (SAW), Allah yana ambaton Annabawa da sunayensu, Ya Adamu, Ya Nuhu, Ya Musa amma babu inda Allah ya kira Annabi Muhammadu (SAW) irin haka. Sai dai wurin da Allah yana so ya yi wani bayani a kansa. Manzon Allah cikamakon Annabawa ne wanda Amnabawa suka yi imani da shi.
“Mu nisanci abubuwan da Manzon Allah ya hana, sai mu ƙara soyayya a gare shi. Duk abubuwan da muke yi na maulidi na abinci da yanke-yanke da sauransu saboda soyayyar Manzon Allah ne. Allah ka ba mu kuɗi fam taɓa sama duk mu kashe su a daren maulidin Manzon Allah (SAW).. Alhamdu Lillah, yau maulidi ya zama alama ta ‘Yan Faila. Kuma yadda ake yi da karatuttuka daga wurinsu aka gani. A da takutaha rabbi rabbi ake yi, a shafa sai baɗi kuma Alhamdu Lillah bisa imani suke yi don girmama Manzon Allah (SAW).” Ya bayyana.
Da yake ƙarin haske a kan waɗanda suke ganin ana ɓata kuɗi a dare ɗaya saboda maulidi domin su, suna ganin sun waye, Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya bayyana cewa hidimar da ake yi koyi ne daga magabata, “Shehu Tijjani bin Usman ya ce da kansa ya taɓa ƙirga shanun da Shehu Ibrahim ya yanka a gabansa (ban da waɗanda aka yanka kafin ya zo Kaulakha) na maulidi a 1949 sun kai 76. To mu me muke yi yanzu? Ba za ka zo da wata wayewa ba ta hana wannan. Da imani mutum zai yi hidima irin yadda Sahabbai suka yi har kafiran Makkah suka riƙa cewa ‘yanzu mu ma yi imani kamar yadda wawaye suka yi?… Don haka ba za ka ce za ka bi Annabi da wayewa (irin taka) ba, haka ba za ka bi Shehu Tijjani da wayewarka ba, haka kuma Sahibul Faidhati Shehu Ibrahim ba za ka ce za ka bi shi da wayewarka ba. Da imani ake yi.
“Mu yi ƙoƙari da alheri, mu kauda kai ga sharri. Mu kawar da kai ga waɗanda suka jahilci abinda muke kai, mu ɗau cutar halitta, babu wata rayuwa da mutum zai yi ya ce ba za a cuce shi ba. Mu kauce wa jayayya, mu kauda kai ga masu mana ƙage, mu yafe. Sannan mu riƙe harshenmu iya iko domin harshe ƙaramin nama ne amma mai girbo bala’i. Shi ya sa aka yi masa katanga da haƙora amma duk da haka sai ya buɗe ya yi ɓarna. Da zaman lafiya da kyakkyawan ɗabi’u Allah ya yaɗa addinin Manzon Allah (SAW). Allah ya haɗa kawunanmu gaba ɗaya.
“Haka nan Shehu Ibrahim ya buƙace mu, mu fitar da cuta biyu daga zukatanmu. Cuta ta farko son duniya, ta biyu tsoron mutuwa, mutum ba zai mutu ba sai kwanansa ya ƙare. Mu sanar da yaranmu harshen larabci, yaren addininmu. Sai dai a yau, akwai masu fassara larabcin da abin da yake kansu (ƙwaƙwalwarsu) ba tare da bayar da haƙƙin ma’ana ta harshen ba. Idan mutum ya iya ƙur’ani ya iya larabci babu wanda ya isa ya ɓatar da shi. Haka waɗanda suke turanci su ma su iya da kyau, haka ita ma Hausar.
“Shehu Ibrahim ya buƙace mu kar mu bar ‘ya’yanmu sakaka, mu ladabtar da su, mu karantar da su iya ƙarfinsu. Kuma ban da dukar da za ta cutar da su. Idan kai kana aiki ba ka da lokacin tarbiyya, ka haɗa yaron da wanda ya dace, sannan idan ka ga yana ƙoƙarin shiga wani alheri kar ka hana shi, domin sai ya faɗa wata hanyar mara kyau.
“Shehu Ibrahim yana mana wasiyya, mu kiyaye farillai da sunnoni, mu tsayar da sallah da zikiranmu da wuridanmu. Mu riƙa faɗar alheri. Mu nemi arziƙinmu, duk abin da mutum ya nema da niyya mai kyau sai ya zama na Allah.
“Don haka Ahlul Faidhati, wanda yake da ikon noma ya yi, wanda yake da ikon kiwo ya yi, haka ma’aikaci da ɗankasuwa ko siyasa. Siyasa alheri ce idan aka kiyaye addini da zaman lafiyar ƙasa.” In ji Shehu Ism’ila.
Tun da farko da yake jawabin maraba da baƙi, jagoran Ahlul Faidhati Mai Diwani Group, Reshen Sakkwato, Sayyadi Abubakar Sakatare, ya gode wa dukkan mahalarta taron maulidin bisa amsa gayyatar da suka yi musamman babban jagora, Shehu Isma’ila Mai Diwani.
Ya ƙara da cewa, duk waɗannan nasarorin da suke samu na shirya Maulidin da sauran karatuttukan da suke gabatarwa daga kyakkyawan zaton da iyayensu suka yi musu ne, kana ya tabbatar musu da cewa cikin yardar Allah sai dai abin ya ci gaba amma ba za a ga akasin haka ba.
A halin da ake ciki, Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya yi wata ƙwaryaƙwaryar tattaunawa da Gidan Talabijin na ƙasa jim kaɗan bayan kammala taron maulidin inda ya yi ƙarin haske a kan alfanun da ake samu a maulidi.
“Mauludin Fiyayyen Halitta yana da alfanu da yawa, yana ƙara sada zmunta, sannan ya koya mana meye ɗabi’un Annabinmu, mu ji halayensa domin Musulmi su yi koyi da shi, idan Musulmi suka yi koyi da halayen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa sallama kamar yadda na baya suka yi koyi da shi, za su koya wa duniya, su ma masu sauran addini su koya wa duniya, domin babu wani addini da zai yi horo da abu mara kyau kowane addini ne. Mu Musulmi mu muke ba da misalai masu kyau da zai zama kowa ma ya ɗauka, to Mauludi duk yana karantar da mu wannan.
“Ga musayar ilimi a tsakaninmu, a yanzu da muka taru akwai mutanen Ghana akwai na Benin, akwai mutanen bangwayen Nijer ɗin nan, kowa yana murna in ya shigo, saboda ya shigo ƙasar addini ya shigo ƙasar alhairai. Mu mu koyi alhairan da suka zo da shi su ma su koyi alhairan da muke da shi.”
Da aka tambaye shi kowane kira zai yi ga Musulmi kan haɗin kai? Shehu Isma’ila Mai Diwani ya ce, “To, mun gode wa Allah, mu bi halayen Annabinmu, mu bi addinmu da kyau da hikima. Meye addini, addini shi ne bauta wa Allah da girmama Allah da bayin Allah, wannan shi ne addini. To idan muka yi riƙo da addininmu muka ji tausayin kanmu, shikenan sai mu zama cikakkun Musulmi, mun yi koyi da addinimu mun yi koyi da Annabinmu, in an dubi Annabinmu, za ka ga haka ne, daga ya bauta wa Allah sai tausayin halittar Allah, don haka ya zama Rahma gare mu duk gaba ɗaya, bauta wa Allah da tausayin bayin Allah.” Ya bayyana.
Daga cikin manyan malaman da suka halarci maulidin akwai Shugaban Tsangayar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usman ɗanfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Yahaya Al-Amin, da Dakta Aminu Abdullahi Sufi, da Malam Lawal Abdullahi Mai Gaskiya, da Shugaban Zakirai na Jihar Sakkwato, Alhaji Abubakar Shugaba da sauransu.