Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki har da abin da ya shafi zamantakewar aure. Kamar sauran makonnin da suka gabata, shafin Taskira ya karbi sakonni daga wajen mabiya shafin, wanda a yau ma shafin ya ci karo da wani sakon, inda aka bukaci boye sunan wadda ta aiko da shi, sakon ya fara da cewa:
“Assalamu Alaikum dan Allah ina so a ba ni shawara, ina cikin tashin hankali, ji nake kamar na kashe kaina. Yau sati na uku da yin aure, amma na ji duk duniya da ban yi auren ba. Wallahi mijina mazinaci ne, yau kwana 4 kenan da na ga abun da idona, wallahi tun ranar da na gani wani jiri ya dauken har yau ba ni da lafiya. Mijina ya fita sallar Asuba sai wuta ta dauke na dauki wayarshi na kunna haske, ina zaune ina Tasbihi kamar da wasa na shiga ‘Gallery’ din wayarsa wallahi hotunan banza da bidiyon iskanci duk a wayar, sai na ga ta WhatsApp aka turo mishi, shi ne na shiga WhatsApp din wallahi ‘yan matan da ya ke ‘charting’ din banza da su sun fi goma. Wallahi a yadda na fahimci chat dinsu da wata a ranar aurenmu sai da ya yi zina, har tana ce mishi ya tafi daurin aurensa ya bar ta cikin ‘sparm’ din shi, wallahi har labarin ‘first night’ dinmu ya bawa wata, wai “salam ya jini?”, wai dan Allah ta shirya tarba gobe zai zo kuma sai da ya je din. Wallahi da na tuna ‘Date’ din tun safe ya fita ya ce mun zai je banki bai dawo ba sai bayan Azahar ashe zina ya je ya yi, wallahi a yadda na fahimta wallahi ba karamin mazinaci ba ne. Ni dai yanzu shawarar da za ku ba ni yadda zan nemi saki ne, saboda wallahi gara na kare rayuwata ba aure da na zauna da wannan mutumin, kuma dukka bai wuce shekara 30 ba, amma ya gama lalata rayuwarshi, kuma ku taya ni rokon Allah ya sa ban dauki cikinsa ba”.
Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin ma’abota shafin, ga kuma bayanan nasu da shawarwari kamar haka:
Sunana Princess Fatima Mazadu Jihar Gombe:
Da farko dai kin yi kuskure, diga wayar mijinki har ta kai ki ga bude ‘Gallery’ dinshi, dan a zahirance haske ki ke so ba ‘Gallery’ ba, kin yi babban kuskure, wanda daga jarida har gidajenmu kallo suna fadakarwa da bude wayar miji. Mafi akasarin mazanmu dole ki same su da dabi’a daya cikin aure-aure; Zina, Luwadi, ko Zamba ko Sata, Nagari, nagartattu ba su da yawa wadanda za su yi samartaka har su gama rayuwar su ba neman mata. Fada na farko hakuri da sirri a zamanatakewa, sannan ki daina saka ido a lamuransa duk inda k ika ga kamar a gurbace ne sai ki yi saurin gyarawa dan toshe wannan barakar. Magana ta uku ke ta ina za ki fara tunkararsa da a wayarsa kin ga badala? Ko za ki ci gaba da zama da shi a haka ne? Ko ko za ki sami ‘yan matan ki hana su nemansa ko ya nemesu? Ba za ki iya ko daya ba, idan ki ka kuskura ki ka dau na waya ba wanda ba zai miki fada ba daga zuriyarsa da na ki duka, abu daya ya kamata ki yi addu’a ba wai shiga damuwa ba, sai ki bi ‘social media’ ki koyi kissa da lallami da gyaran da karuwan suke yi ke ma ki masa ki lallabashi a nutse a dabarance. Amma fa za ki sha dan fama dan ke ma nagartaccen rayuwa za ki dauko me cike da tari hak’uri da kau da kai. Shawara ta farko kar ki sake daukar wayar mijinki in ba so ki ke ki nakasa ko ki mutu lokacinki bai yi ba, dan ko ba sirri na zina ba koma meye shi yanada iko kan wayar ki dan shi ya auro ki, ke kuma karkashinsa ki ke bai kamata kina duba abun da bai sa ki ba. Na biyu akwai dole abun da k ika gaza dan mata in an aure mu ji muke mun fi na waje koma yaya, wallahi kuskure ne babba, dan dole ku dawo; wawiya, doluwa, karamar yarinya, mai shagwaba, da yarinta, amma sai ki dau kanki ke ma fa kin zamo babba tunda kin yi aure, to waya can kuma maida kansu suke kananan yara su mori mijin naki ki gyara kuma ki je ki kara gyara na amare da yanzu ya dawo ruwan dare, ki rage kishi, ki daina gulma, ki kau da kanki kamar baki ganshi ba ko meye ya ke aikatawa. Ina miki fatan alheri, kar ki taba sanya wa za ki rabu da shi, sai gyara dan ba ki san yadda wasu ke fama ba, gwara ke karya ya ke miki, wata kuma akan gadonta ake yi kuma ta dafa ta basu su ci, su yi wanka ta basu kayanta su saka, ke za ki iya gyara shi in kin gyara tunda lami ya jiki ba wai baya sonki ba.
Sunana Abba Gada Rano Unguwar Liman Gada:
Innalillahi wa inna ilaihirraji’un gaskiya kina cikin tashi hankalin duniya sanan kuma Allah ya soki da rahamarsa abin da ya sa na ce haka shi ne duk mace da ka ce mijinta yana bin Mata to na cikin tashin hankali, kuma abun da ya sa na ce Allah ya so ki da rahamar sa dan ya sanar da ke da wuri. To shawarata anan ita ce; Ba wai rabuwa da auren ne mafita domin idan kuka rabu hakan ba zai sa ya daina ba illah ma ya ci gaba kuma ba mamaki rashin Auren ne ya sa shi yin zina din, to tunda kin gane hakan to sai kisa shi a cikin addu’a, kuma duk wani abu da zai sa hankalinsa ya kai kan wata mace ki yi kokarin dauke masa kuma ki zauna da shi ke matar sa ce, ki nuna masa kin zo ne dominsa ya hakura da duk wata mace tun da ga ki, Allah ya kara shiryar da mu.
Sunana Sunana Musbahu Muhammad Gorondutse:
Da farko dai tayi kuskure, ta ce tana tasbihi kuma ta shiga ‘Gallery’ daga nan ta shiga Whatssapp, amma abin da ya kamata tayi shi ne ta sanar da iyayenta su kira shi su yi magana da shi akan abin da ya ke faruwa, idan akwai yiwuwar sasantawa sai ayi kuma ayi masa fada da addu’a. Sannan ya kamata ayi ‘Medical Test’ kafin su koma rayuwar Aure da shi. Allah ya shiryar da shi ita kuma Allah ya bata mafita.
Sunana Abdullahi Adamu Gwani (Mai Nasara) Gama Karamar Hukumar Nassarawa Jihar Kano:
Ni kuma a tawa mahangar ita ce tabbas tayi kuskure saboda bunciken da tayi a wayarsa ne ya nuna mata hakan, amma tabbas rabuwa da shi shi ne mafita a gare ta, domin dogaro da wata aya a cikin suratul Nur aya ta 3 inda Allah ya ke cewa; “Mazinaci baya auren kowa sai mazinaciya ko mushrika, ita ma Mazinaciya ba ta auren kowa sai Mazinaci ko mushriki, an haramta musu auren mumini”. To kuwa tunda ita ba halayyarta bace ba tada hadi da shi ya je ya nemi irinsa Allah ya sa mu dace.
Sunana Auwalu Abdullahi Umar Kiru, Kiru LGA Jihar Kano
Shi dai aure daya daga cikin sunnar fayayyen halitta Annabi Muhammed (SAW) ne, wacce ta dabbaka kuma ya umarci mabiyansa duk duniya su yi koyi ko su dabbakata idan har suna da hali/sukuni/dama su aura daga biyu, uku ko hudu idan kuma ba za su yi adalci ba su auri guda daya. Sannan zina wata hanya ce ta sabon Allah wacce muhallicimu, Allah (SAW) ya haramata. Inda a cikin littafinsa mai tsarki ya ke cewa; “Kada ku kusanci zina, ma’ana ba ma kada ayi ta ba, kusantar da kai ko yunkurin yi wani abu da zai kai ka ga yi haramun ne. Ya Allah ya ci gaba da kare mu baki daya. ‘Yar uwa, Allah da ya hallitta aure ya kuma halitta saki sai dai baya son ayi shi domin hatta al’arshinsa sai ta girgiza a dalilin rabuwar aure. Ina mai amfani da wannan damar na roke ki arzikin hakuri da bin wadannan hanhoyin da zan zayyano alarshi idan bai yi nasara ba, sai akai ga abin da ba ma so wato ‘saki’. Zama da shi ta lallama da fadan abin da addini ya fada akan ma’aurata da hakkin juna, tura magana ga magabat (Waliyyai da wakilai), Addu’o’i da gurfana a gaban Allah ako da yaushe, shigo da malamai cikin maganar don su dada jaddada sakon Allah (SWA) sai kuma kai wa ga hukuma idan duk abin da muka zayyana sun ki bada masalaha. Allah ya kiyaye, ya ‘yar uwa da duk masu irin wannan lalurar mu ci gaba da kaskantar da kai a gaban Allah da kuma neman taimakonsa ako wanne lamari ba sai aure ba. Gare ki y’ar uwa, .Idan Allah ya sa an sami nasara ya daina waccen mummmunar dabiar da ma haka addnini ya ke so idan kuma ta kai da rabuwa to ke ma sai ki gaggauta aure domin kin yi auren zai jefa ki cikin zargi wanda babu wanda ya isa ya hana hakan. Ya Allah ya kara kare mu daga fadawa mummunar kaddara, Ameen.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi:
A gaskiya wannan miji shi ake kira gwara babu, Shawarata anan ita de; ire-iren masu aikata hakan ya kamata su san cewa su ma fa wataran iyayye ne, kuma za su haifi yara ace ‘Yar wani ta aure miji mai wannan hali dan Allah maza musamman masu aure sun fi samari aikata haka, ke kuma shawarata gare ki shi ne ki yi hakuri, sannan ki fadawa iyayyenki da nashi iyayyen, sannan muma za mu taya ku da adduwa Allah ya kawo miki sauki cikin lamarin, su ma ‘yan mata da suke biye wa bukatun samari Allah ya ganar da su a wannan lokacin adduwa ce kadai mafuta, dan Allah ya kamata in za ayi aure a tsananta buncike kamar yadda addinin muslunci ya tanadar Allah ya cire ki daga wannan ta shin hankali.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano KNARDA:
Ya salam kaico da wannan rayuwa ta ‘yan wannan zamani, Maganar gaskiya wannan ba karamin abin wasa bane sannan tunda an riga da an daura muku aure kamata ya yi ke ma ki rike sirrinki domin wannan sirrinki zan ce tunda shi bashi da rike sirrin tunda har ta kai ga yana fadawa wata fasika sirrinsa yadda ya sameki. Sannan babbar shawarata a gare ki da sauran maza da matan masu yawan duba wayar abokan zamansu mu kara kula da kiyayewa muna hakuri da duba wayoyin, sabida gudun gano bacin rai. Sannan shawarata ta karshe anan ita ce kada ki fara gayawa kowa shi ma idan baki nuna masa kin gani ba ki sake samun lokaci sai kiyi ‘forward’ din duk abin da za ki iya wanda ya ke daga cikin halinsa na banza, sannan ki yi ‘screen short’ a wayar ta sa sai ki tura a taki wayar, sannan sai ki gayawa waliyansa da naki sai a san yadda za a yi a magance matsalar Allah ka kara yi mana tsari da munanan halaye kashirye mu da zuri’ar mu baki daya ameen.