Safara’u Sani, mai ‘Precious Annur SF cosmetics’, tana daga cikin wadanda suka samu tallatawa a wajen wasu bankuna wanda ya taimaka ta bunkasa kasuwancin ta a cikin kankanin lokaci.
A cikin wannan tattaunawa da Jaridar LEADERSHIP Hausa, Safarau ta yi magana kan juya karamin jari zuwa sana’a mai inganci, ta kuma bayyana cewa rashin isasshen jari a harkokin kasuwancinta na haifar da kalubale a kasuwanci. Ta nemi goyon bayan manyan kamfanoni masu zaman kansu da gwamnati zuwa ga kananu da matsaikacin kasuwanci (SMEs) don taimakawa a wajen yaki da talauci.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Kudin Sufuri Da Kashi 40 Ta Hanyar Amfani Da Motoci Masu Iskar Gas
- Kudin Ajiyar Sin Na Ketare Ya Karu Da Kaso 0.86 Cikin Satumba
Wane irin kasuwanci kike ciki?
Ina Kasuwanci na sarrafa man shafawa da baseline.
Me ya sa ki ka zabi wannan layin kasuwanci ba sauran kasuwancin ba?
Saboda shi ne Kasuwancin danaga nafi iyawa, kuma naga zan iya yi har na taimaka wa ‘yan uwana mata da matasa dan samun ci gabansu.
Yaya riibar wannan kasuwancin yake?
Ina samun riba tayawan kayan da muka sarrafa da kuma yadda kasuwa ta karbi kayan.
Ta yaya ki ka tara kudi / jari don fara wannan kasuwancin?
Na fara ne da karamin jari dana tara dubu goma sha biyar, (N15,000) Allah ya sa albarka a ciki har na kai wannan matsayi da nake a yau har ina sarrafa katan dubu goma. (10,000) Cartons.
Akwai wani banki da ke da hannu a ci gaban kasuwancin ki?
Eh, Bankin Jaiz Bank da ya sayamin kayan dazan sarrafa kasuwancina ta aro zuwa SME, kuma ina matukar alfahari da Jaiz bank, san nan ina kara gayawa yan kasuwa da sauran mutane akan taimakon da Jaiz bank ya yi.
Kina amfani da wani App na Bank a waya don kasuwancin ki?
Ina amfani da App na Jaiz bank, tare da na First bank.
Mene ne kalubalen da ake fuskanta a kasuwancin ki?
Babban kalubalena rashin jari mai karfi, yadda ba dan shigowar Jaiz bank cikin kasuwancina ban san yadda zan yi ba, amma duk da haka jarina ya yi kadan idan na duba yadda kasuwa ta karbi kayan da muke yi.
Wane dabaru kike sanyawa kan kalubalen?
Ina sa dabaru ta karbar order wajen ‘yan kasuwa da mutane su bamu kudi kafin mu yi musu production na kayan da suke bukata.
Me kike ganin ya kamata bankuna su yi don taimakawa kananan yan kasuwa su karu, da magance talauci a Najeriya?
Muna son bankuna su dinga shiga cikin kasuwancin kananan yan kasuwa ta hanyar saya musu kayan da suke kasuwancin, don a samu ‘yancin kai, kuma mu yaki talauci da rashin aikin yi.
Mene ne shawarar ki ga matasa ‘yan kasuwa masu son fara kasuwanci?
Shawara na shi ne su tsaya a kan abin da suke Kasuwanci akansa, san nan komai kankantar jarinsu in suka dage zai zama babba, kamar ni da jarin dubu sha biyar na fara da, Allah ya taimakeni ya sa albarka 5a ciki.
Mun gode
Nima na gode