Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana yadda gwamnatinsa ta warware yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi na tsawon watanni hudu a rana daya.
Ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Abuja, a wajen bikin cika shekara 70 na Bishop Mathew Hassan Kukah, na darikar Katolika na Sakkwato, wanda cibiyar Kukah ta shirya.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan IPOB 2 A Imo
- Tauraron Dan Adam Na Farko Na Binciken Hasken Rana Na Kasar Sin Ya
LEADERSHIP Hausa, ta ruwaito cewa malaman jami’o’in sun shiga yajin aikin ne tun a watan Fabrairu saboda rashin jituwar da ke tsakaninsu da gwamnatin tarayya.
“Al’ummar da muke tafiyar da su na da sarkakiya, yanzu maganar yajin aikin ASUU muke yi, a lokacina ma ASUU ta yi yajin aikin na tsawon watanni hudu, kwamitoci daban-daban sun yi taro amma babu abin da ya yi aiki. Na ce ta yaya yaranmu za su daina zuwa makaranta har tsawon wata hudu? Don haka sai na kira taro na dukkan shugabannin kungiyar ASUU.
“Na jagoranci taron da kaina, mataimakin shugaban kasa yana, Antoni-Janar na tarayya shi ma yana nan. Miinistocin ilimi suna nan, ministocin kwadago akwai ministocin kudi, duk wanda ke da alaka da taron yana nan.
“Kuma na yi tunanin cewa kasancewata a wurin zai taimaka mana mu yi abubuwa da sauri. Amma sai da muka kwana har zuwa misalin karfe 5:30 na safe kafin mu kammala kawo karshen yajin aikin, don haka akwai matsaloli,” inji Jonathan.
Ya bayyana cewa duk da alakar da Bishop Kukah ke da ita da shugabanni hakan bai hana ya soke su ba, a duk lokacin da yake ganin sun yi ba daidai ba.