Fitaccen Jarumin fina-finan Hausa, wanda tauraruwarsa ke haskawa cikin masana’antar Kannywood, Jarumi, Mai shiryawa, Mai Bada Umarni, Marubucin fina-finan Hausa, kana Shahararren mawaki. IBRAHIM BALA wanda aka fi sani da UMAR cikin shiri me dogon zango na Labarina, ya bayyana wa masu karatu tsawon shekarun da ya shafe yana rubuta waka da kuma rerawa, wanda hakan ya kasance tun kafin bayyanarsa matsayin Jarumi. Jarumin ya kara da bayanai masu yawan gaske game da bayyanarsa matsayin mawaki, inda ya yi karin haske game da rikidewarsa daga Jarumi, Mai Bada Umarni zuwa Mawaki. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Darakta Ibrahim Bala ta ya ka tsinci kanka a matsayin Mawaki, me ya ja hankalinka har ka tsunduma harkar waka?
Tun ina islamiyya nake irin wakokin maulud saboda ina da ra’ayin waka sosai, saboda tana iya isar da sako cikin kankanin lokaci.
Ma sha Allah, a yanzu kana ci gaba da yin wakokin yabo ne kamar na islamiyya ko kuwa canja akala daga yin irin wadannan wakokin?
Ina yin na yabo, sannan ina rubutawa, ina wakokin siyasa da na sarauta, talluka da sauransu, amma ban fiya yin wakokin soyayya ba.
Kai kake rera wakokinka ko kuwa rubutawa kake yi ka bayar a rera?
Duka ina yi, amma nafi rubutawa.
Kasancewar ka fara da kasidu tun daga islamiyya, shin ka nemi taimakon wani ko wata a wancen lokacin da za ka fara rubuta wakar ko kuwakai tsaye da kanka ka fara?
Ban nemi tamakon kowa ba bayan na saurari wakoki sosai, an kuma rera wasu dani a haka na fara gwadawa sannan na nemi taimako. Malamai sun taimaka sosai, idan na rubuta muna bayarwa wasu malaman a lokacin suna duba mana.
Wanne abu ne ya fara baka wuya lokacin da za ka fara rubuta waka?
‘Kafiya’ saboda duk yadda ka kai baitUkanka dole sai ka nemo ‘Kafiya’.
Ya batun wajen rera waka fa, shin ka fuskanci wani kalubale daga bangaren, musamman yadda za ka ji wasu na cewa sun sha wuya wajen dora waka wani ma har ya kusa kuka, ya abin ya kasance a gare ka?
Na sha wuya sosai kuwa.
Bayan da kake wakar islamiyya ajjiye wakar kayi daga baya ka dawo ka ci gaba, ko kuwa tun lokacin da kake yin ta islamiyya kawo iyanzu kana ci gaba da wakar ba tare da ka daina ba?
A lokacin har koyarwa nayi amma gaskiya yanzu mun bar islamiyyar.
Daga lokacin da ka fara waka kawo iyanzu za ka yi kamar shekara nawa da faraway?
Shekara goma sha wani abu, an doshi ashirin, domin tun kafin na san mene ne waka, tun ina karami soaai.
Idan na fahimce ka daidai, kank so ka ce ka fara waka tun kafin ka fara harkar fim kenan?
Kwarai tun ban san fim ba na fara wakar islamiyya.
Da wacce waka ka fara bayan ta ismaliyya da kake yi?
Da wakar fim na fara a lokacin.
Ya sunan wakar kuma ya amshin wakar yake, me wakar ta kunsa?
Tambalili muyi rawa mu cashe ‘Yar gala galar soyayya.
Ka yi wakoki sun kai kamar guda nawa?
Nayi wakoki sun kusa 50.
Ko za ka fadowa masu karatu kadan daga ciki?
Yawanci na sarauta, siyasa, ne bana fim ba, amma ta fim an sa cikin wani tsohon fim INIBI, Darajar So, da kuma wani sabon series da ake dauka a yanzu ‘Auren Soyayya’.
Wasu mawakan na yin amshi da mata har da wasu baitukan, wasu kuma su suke yin amshinsu da baitukansu ba tare da sun saka mata ba, shin kai wanne ka fi yi?
Duk mun yi mun bada baituka, mun bada amshi. Wata nayi ni kadai, wata wakar ni da mace.
Da wacce mawakiya ka fi yin waka?
Murja Baba ita ce mawakiyar da mukai wakoki.
Wacce waka ce cikin wakokinka ta zamo bakandamiyyarka, wadda kafi so, da wadda al’umma suka fi saninka da ita?
Ba ta fim bace ta sarauta ce na yabi wani.
Ya sunan wanda ka yaba ko sirri ne?
Sirri ne amma Sarkin Fulani ne.
Jama’a da dama za su yi mamakin kasancewarka mawaki musamman yadda kowa ya sanka matsayin jarumi, ko marubucin fim ko kuma mai bada umarni, me za ka ce akan hakan?.
Da farko na fara waka ne a Kannywood sabida muna neman me ya kamata muyi a lokacin, ba ma samun aiki kuma na taso ‘Nagudu Inbestment’, a haka muka fara wakar daga baya da fim yayi rinjaye sai muka jingine waka sai jefi-jefi muke yi.
Bayan da ka fara waka me mutane suke fada a kai?
Wasu dama sun sanni a ‘Studio’ ba suyi mamaki ba, wasu kuma su ce zan iya saboda ina da sa abu a rai.
Ya ka dauki waka a wajenka, kasancewarka Jarumin fim?
Wata hanya ce ta isar da sako cikin kankanin lokaci.
Wanne nasarori ka samu game da waka?
Nasarar bata wuce ta yadda kowanne mai sana’a ke samun na kashewa ba.
Ko akwai wani kalubale daka taba fuskanta game da waka?
Akwai lokutan baya na sha wahala kan mata masu dora amshi saboda a lokacin sun fi son waka da wanda yayi fuce.
Kamar da wanne lokaci ka fi jin dadin rubuta waka?
Da Sassafe ko da Yamma
Ko kana da ubangida a harkar waka?
Duk tsofin mawaka iyayena na gida a guna.
A gaba daya ayyukan da kake yi na harkar fim da kuma waka wanne ne ya fi baka wuya?
Bayar da umarni (Directed) aiki ne mai matukar wahala, yana bukatar nutsuwa da sanin yakamata, saboda dukkan kuskure kai ne ba a ganin kuskuren kowa.
Mene ne burinka na gaba game da waka, da kuma burinka na rayuwarka gaba daya?
Burina nayi wakokin soyayya ga manzon Allah (SAW) wakar tayi fuce ko ina a jita, sannan babban burina ba kawai na shahara ba ina so na samu kudi masu yawa yadda zan taimaki iyayena ‘yan uwa da abokaina.
Da wanne mawaki kake son yin waka a nan gaba?
Kowanne mawaki, ina son nayi waka da shi.
Idan mutane na son ka yi musu waka ta wacce hanya za su bi domin su same ka?
Kai tsaye ofishinmu dake kabuga Nagudu Inbestment ko E-mail Address [email protected] ko nema kai tsaye inda muke ayyukan mu.
Ka taba nunawa wasu yadda za su rinka rubuta waka ko kana da sha’awar hakan anan gaba?
Muna zama na gyara musu wakoki kuma ko na rubuta na bayar.
Wanne mawaki ne ya fi birge ka tun kafin ka fara waka da kuma bayan ka fara waka, wanda kake jin da ma ka zama kamar sa?
Mawaki mai faran-faran da mutane wanda baya girman kai.
Me za ka ce da masu sha’awar fara yin waka, da kuma wadanda ke cikin harkar?
Su zauna da wadanda suke aiki su koya, kada su yi girman kai ko su yi abun da ka.
Ko akwai wani kira da za ka yi ga masu sauraron wakokinka?
Su dauki abun da suka ji na fadakarwa su yi amfani da shi, su watsar da kuskure idan sun ji sannan su bani gyara idan da gyara ni mai karbar shawara ne.
Ko kana da wani kira da za ka yi ga gwamnati game da ci gaban mawaka?
Ta taimakawa mawaka suna bukatar tallafi, waka sana’a ce da za ta rike mutane ta kuma taimake su.
Me za ka ce da masoyanka?
Ina son su fiye da yadda suke sona saboda su nake yin komai.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Masoyana baki daya suna da dimbun yawa nan ba zai dauki adadinsu ba.