Tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Super Eagles sun sami nasara akan abokan karawarsu, kasar Mozambique da ci 3-2.
Wasan wanda aka buga a kasar Portugal, ya kasance wasa na biyu a cikin kwana hudu da Super Eagles suka buga.
- Arsenal Ta Nuna Sha’awar Daukar Osimhen Idan Ya Yanke Shawarar Barin Napoli
- Nijeriya Da Saudiyya Sun Yi Kunnen Doki A Wasan Sada Zumunta
Teran Moffi, Frank Onyeka da Moses Simon ne suka jefawa Super Eagles kwallo a ragar Mozambique.
Kocin Super Eagles, Jose Peseiro, ya yanke shawarar saka mai tsaron raga Francis Uzuho duk da sukar da akeyi masa tun bayan wasansu da kasar Saudiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp