Bisa wani nazarin bincike da kafar yada labarai ta Reuters ta gundar ya nuna cewa, Nijeriya ta kara yawan man fetur da take hakowa zuwa ganga 70,000 a kowace rana, wanda hakan ya haura fiye da adadin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC+ ta sanya mata.
A cewar wannan nazarin na Reuters, a watan Fabirairun 2025, OPEC ta hako Gangannan Manfetur miliyan 26 da 74,000 a kowace rana.
- Majalisa Ta Umarci NCC Ta Rufe Dukkanin Shafukan Intanet Na Batsa A Nijeriya
- Hajjin Bana: NAHCON Za Ta Fara Jigilar Maniyyata A Ranar 6 Ga Mayu
Nazarin ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa, an samu karin Gangunan Manfetur da suka kai 170,000 a kullum, idan aka kwantanta da watan Janairun 2025.
A cewar binciken, hasashen da kungiyar OPEC+ ta yi a watan Fabirairu ya karu, a ya yin da Man da kasar Iran ta fitar ya karu, duk da yunkurin da kasar Amurka ta yi na dakile fitar da shi, wanda hakan ya sanya Man Nijeriya ya karu, ya kuma dara daidai da hasashen da kungiyar OPEC+.
Kasashen da suke cikin kungiyar OPEC+ da suka hada da kamar kasashen Rasha da sauran kawaye, sun nuna bukatar ganin an rage yawan Manfetur din da suke hakowa a watan Maris na 2025.
Sun nuna wannan bukatar ce, biyo bayan hasashen raguwar bukatar Manfetur din da kuma dabarar fitar da shi, daga kasashen da ba sa cikin kungiyar ta OPEC+.
Sai dai, a ranar Litinin da ta gabata kungiyar ta tsaya daram kan tsarinta na kara yawan Man da ake hakowa a watan Afirilu.
Kazalika, binciken na kafar Reuters ya kuma gano yawan adadin karuwar Man na OPEC wanda ya kai Ganguna 80,000 da suke fitowa daga kasar Iran wanda ya kai Ganuna miliyan 3.30, wannan ya kai daidai na alkaluman watan Satumba, wanda ya haura tun a 2018.
Bugu da kari, binciken ya sanar da cewa, fitar da danyan mai daga Iran ya farfado lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden duk da takuntuman kasar Amurka, sai da karkashin shugaban kasar Amurka Donald Trump, na sabunta kokarinta.
Sauran Man na biyu na fitowa ne daga Nijeriya, inda yawan Man da take fitawa ya karu kuma yawan bukatarsa a cikin gida ta karu saboda samar da Matatar Mai ta Dangote.
Hakazalika, bincken na kafar Reuters, ya gano cewa, yawan Man da manyan kasasshe biyu da suke a cikin kungiyar OPEC wato Saudi Arabia da Irak, na su ya ragu, inda a yanzu suke hako kasa da wanda OPEC+ ta sanya masu su hako.
A cewar nazarin, man da kasashe mambobin kungiyar OPEC suka fitar a watan Fabrairun 2025 ya karu, inda Iran ke kan gaba, duk da kokarin da kasar Amurka ta yi na yunkurin dakile fitar da man.
To sai dai a ranar Litinin, ta yanke shawarar dakatar da shirin nata, inda take sa ran kara yawan man da take hakowa a watan Afrilu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp