A wani gagarumin mataki na bunkasa harkokin diflomasiyya tsakanin Sin da Nijeriya, a kwanan nan ne gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) ya sanar da shirin fara watsa shirye-shirye cikin harshen Sinanci ko Mandarin a Turance. Wannan yunkuri da Darakta-Janar na VON Jibrin Ndace ya bayyana a kwanan nan yayin wata ziyarar da ya kai ofishin jakadancin Sin a Nijeriya, yana nuna wani muhimmin sauyi ne mai ma’ana da za a samu a huldar Nijeriya da Sin.
To amma wane muhimmanci hakan yake da shi? Amsar ita ce, ta hanyar fassara labarunta tare da watsawa da Sinanci, Nijeriya za ta bude wata sabuwar kafa ta isar da sako ga al’ummar da take da yawan jama’a a duniya. Sannan masu zuba jari na kasar Sin, da jami’an diflomasiyya, da sauran Sinawa dake da sha’awar zuba jari a tattalin arzikin Nijeriya za su rika samun sabbin bayanai kai-tsaye a cikin harshensu na asali. Wannan zai kara kawar da shingen yin cudanya da juna, kana dimbin Sinawa za su fahimci sauye-sauye da ci gaban da ake samu a Nijeriya. Kuma tabbas, wannan zai karfafa amintattun abubuwan hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a mataki na yanki da kuma na kasa da kasa.
- Za A Watsa Shirin Talabijin Don Bayyana Tunanin Al’adu Na Xi Jinping
- Rundunar NSCDC Ta Kama Wani Da Ake Zargi Da Hada-hadar Miyagun Kwayoyi A Kano
Kazalika, wannan yunkuri ya nuna yadda Nijeriya ta fahimci alfanun da ke tattare da rungumar kasar Sin da gudanar da hadin gwiwa tsakanin kafofin yada labarai na kasashen biyu wanda aka rattaba wa hannu a gefen taron FOCAC da shugaba Tinubu ya halarta a birnin Beijing a bara.
Bugu da kari, kasancewar kamfanonin kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa ababen more rayuwa a Nijeriya, fara watsa shirye-shirye da Sinanci zai yi tasiri ga zurfafa hadin gwiwar sassan tattalin arzikin kasar ta hanyar zama gadar sadarwa da kara fahimtar abubuwa a kan lokaci musamman masu nasaba da bunkasa layin dogo, tituna, filayen jiragen sama, makamashi da sauransu.
A fannin noma ma, watsa shirye-shiryen da Sinanci zai taimaka wajen bayyana burin Nijeriya na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, musamman yadda take neman aikewa da karin kayayyakin amfanin gona zuwa babbar kasuwar kasar Sin, tare da bai wa masu ruwa da tsaki na kasar Sin damar sanin abubuwan da Nijeriya za ta iya yi, da ka’idojinta ta yadda hakan zai kara daidaita al’ummomin kasashen biyu kan dabarun kasuwanci da kara habaka musayar noma.
A halin yanzu, masana’antun kirkire-kirkiren fikira da na fina-finai, da na kayan kwalliya, da kide-kide da wake-wake suna taka rawar gani wajen harkokin al’adu da kasuwanci. Watsa shirye-shirye da Sinanci zai bai wa masu ruwa da tsaki a wannan fani na kirkire-kirkiren fikira na Nijeriya damar yin cudanya da takwarorinsu Sinawa kai-tsaye, da inganta fahimtar al’adu da yaukaka zumuncin diflomasiyya musamman ma bisa yadda kasashen biyu ke daraja al’adun gargajiya da bayar da labarai na al’mara da hikayoyi. Tabbas, wannan bangare na Nijeriya zai samu tagomashi mai albarka ta fuskar hadakar shirye-shiryen fina-finai, da bukukuwan nune-nunen, da kuma fadada samun kasuwa.
Har ila yau, yayin da Nijeriya ta shiga cikin kungiyar mawaka masu rajin ganin dunkulewar harsuna da tabbatar da damawa da kafofin watsa labaru daban-daban a duniya, watsa shirye-shiryenta da harshen Sinanci zai taimaka wa ayyukanta na diflomasiyya a fannonin tattalin arziki, da cudanyar al’adu, da hadin gwiwar manyan tsare-tsare. Don haka, watsa shirye-shiryen Nijeriya da Sinanci ba kawai bangare ne na yada labarai ba, wani babban yunkuri ne na cin moriyar samar da duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp