• English
  • Business News
Saturday, May 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (4)

by Idris Aliyu Daudawa
10 months ago
in Ilimi
0
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (4)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kwalejin ilimi ba su yin abinda ya dace saboda ba a basu wani muhimmancin da ya kamata ba, hakan ma shi yasa lamarin koyarwa ya kasance wuri na karshe na wadanda suka kammala jami’a ba su kuma sha’awar aikin koyarwa,ba su kuma a shirya su koyi yadda za su koyar yadda ya dace.Domin kuwa suna yin aikin koyarwa ne kawai domin su samu hanyar biyan bukatunsu.

Shi ya sa masu makarantu ba shirye suke ba su rika basu albashin da ya dace ba,saboda yadda suka dauki malaman makaranta ba da wata daraja ba.Haka lamarin yake sai dai kuma ba a taru aka zama daya ba.

  • Sufeton ‘Yansanda Ya Amince Da Zanga-zangar Matsin Rayuwa, Ya Gindaya Sharadi
  • Muhimmin Sakon Kwankwaso Ga ‘Yan Nijeriya Kan Shirin Zanga-zanga 

Alalade ya kara yin bayani inda yake cewa rashin isassun malaman makaranta abin ba ya tsaya kadai bane kan Lissafi da Turanci,a takaice dukkan darussan.“Daga cikin ‘ya’yanmu namu muke son su zama malaman makaranta? Iyaye nawa suke fatan ‘ya’yansu su zama malaman makaranta? Makarantu nawa ko manyan makarantu suke koyarwa da manufar jan hankalin ‘yan makarantar su yi sha’awar aikin koyarwa?

Abin so ne a a daukaka darajar malaman makaranta ta kasance irin ta ma’aikatan Banki ko kuma masu aiki a kamfanin mai,domin yin hakan zai iya sa abubuwa  a canza yadda ake Kallon malaman makaranta, daga haka kuma za a fara ganin sauyi daga yadda suke gudanar da aikinsu.Muna sa ‘ya’yanmu amakaranta ne domin su yi aikin da bai danganta da koyarwa, idan kuma ba mu yi haka ba maganar karancin malamai a darussan Lissafi da Turanci abin zai kara kazancewa ne.Lukaci ya yi wanda dole ne sai mun canzawa matasa yadda ya dace da kamata su kaunaci aikin koyarwa da su malaman makaranta.

Kamata ya yi a fara yanzu domina sauya tunanin wasu dalibai su rungumi aikin koyarwa saboda a gaba a samu wadanda  za su yi aikin bilhakki da gaskiya.Dole ne a samo mafita na tsaro da wasu manufofin da sharuddan da za su jan hankalin wadanda basu sha’wara yin aikin malamain makaranta su yi sha’awar haka.Sai dai tambayar ita ce wanene, ko kuma me zai koyawa ‘ya’yanmu da jikokinmu  idan ba a yi tsarin da abin zai jawo hakali ba, ai zai wuyar ka tallata abinda ba ka tanada ba!”

Labarai Masu Nasaba

Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China

Makafi 37 Sun Zana Jarabawar JAMB A Bauchi

Iyaye da basu son ‘ya’yansu  su zama malaman makaranta

“Akwai abin da ke  bada gudunmawa wajen rashin isassun malaman da za su koyar a darussan Turanci da Lissafi. Abin mamaki shi ne iyaye na bukatar a koya wa ‘ya’yansu amma basu bukatar ‘ya’yansu su zama malaman makaranta.Ko wa ai ya san dalilin domin kuwa iyaye sun bar maida hankali a kan irin kokarin da ‘ya’yansu suke yi kamar yadda ya dace tun da farko su yi hakan.Ba su damu ba koma wanene zai koyawa ‘ya’yansu, su kawai abin da suke bukata ‘ya’yan su kasance sun samu zuwa ajin SS2.

Daga nan kuma sai ta wacce hanya ‘ya’yan nasu za su rubuta jarabawa sanin kowa ne kuma irin haka ne har sai aki ga  bata lokaci  saboda lokaci ya kure.Ya dace iyaye su maida hankali kamar yadda ya dace dangane da lamarin ilimin ‘ya’yansu.Su bada duk wata gudunmawar da suka za ta taimaka wajen ilimin da ‘ya’yansu za su samu mai nagarta,matukar idan har basu bukatar a rika ba ‘ya’yansu duk abin da aka ga dama da suna albashi,idan ba fata da bukatar kaiwa ga haka, a kula da malaman makaranta wajen biyansu albashi mafi tsoka ta haka ne ‘ya’yanku da jikokinsu za su samu ilimi mai inganci.”


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: EducationIlimi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Ake Alale Mai Kwai

Next Post

Amfanin Almiski Da Sabulunsa (2)

Related

Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
Ilimi

Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China

2 weeks ago
Makafi 37 Sun Zana Jarabawar JAMB A Bauchi
Ilimi

Makafi 37 Sun Zana Jarabawar JAMB A Bauchi

2 weeks ago
Gwamnatin Tarayya Ta Umurci WAEC, NECO Su Koma Amfani Da CBT Nan Da 2026
Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Umurci WAEC, NECO Su Koma Amfani Da CBT Nan Da 2026

2 weeks ago
Nijeriya Ta Biya Bashin Ɗaliban Da Ke Karatu A Ƙasashen Waje
Ilimi

Nijeriya Ta Biya Bashin Ɗaliban Da Ke Karatu A Ƙasashen Waje

2 weeks ago
Dalilai 12 Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmanci Ga Al’umma (2)
Ilimi

Dalilai 12 Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmanci Ga Al’umma (2)

3 weeks ago
Fursunoni 62 Sun Rubuta Jarrabawar NECO da MBAIS A Kano
Labarai

Fursunoni 62 Sun Rubuta Jarrabawar NECO da MBAIS A Kano

3 weeks ago
Next Post
Amfanin Hulba 21 Ga Lafiyar Dan’adam (2)

Amfanin Almiski Da Sabulunsa (2)

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu

Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu

May 10, 2025
Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

May 10, 2025
Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

May 10, 2025
Zulum Ya Haramta Sayar Da Fetur A Bama Don Yaƙi Da Ta’addanci

Zulum Ya Haramta Sayar Da Fetur A Bama Don Yaƙi Da Ta’addanci

May 10, 2025
Rikicin Filato Ya Sa Makiyaya Yin Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Wata 2

Rikicin Filato Ya Sa Makiyaya Yin Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Wata 2

May 10, 2025
Malaman

ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda

May 10, 2025
Ƙungiyar Sadarwa Ta Ƙasa Ta Fitar da Sabbin Matakan Tallata Nasarorin Gwamnatin Tinubu

Ƙungiyar Sadarwa Ta Ƙasa Ta Fitar da Sabbin Matakan Tallata Nasarorin Gwamnatin Tinubu

May 10, 2025
Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi

Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi

May 10, 2025
Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet

Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet

May 10, 2025
Mambobin APC Sun Buƙaci EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Matawalle

Mambobin APC Sun Buƙaci EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Matawalle

May 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.