Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacimmu na yau zai yi duba ne game da hadarin rashin tsaftar cikin gida. Ga dai ra’ayoyin masu karatunmu kamar haka.
Usman Sani
Rashin tsaftar cikin gida yana haifar da kananan cututtuka ta hanyar jawo yaduwar kwayoyin cuta, kamar su kwayoyin da ke haddasa ciwon ciki, zazzabi, da gudawa. Wuraren da ba a tsaftace ba suna jan hankalin kwari da dabbobi masu dauke da kwayoyin cuta.
Wadanne hanyoyi za a bi don magance su?
Za a iya magance cututtukan da rashin tsafta ke haifarwa ta hanyar tsaftace muhalli akai-akai, amfani da ruwan sha mai tsabta, da tsaftace hannaye kafin cin abinci da bayan amfani da bayan gida. Haka nan, sanya shara a wuraren da suka dace da kuma tsaftace jikin dabbobin gida na taimakawa.
Sajida Ahmad Ibrahim
Assalamu alaikum. Cutittikan da rashin tsaftar cikin gida take haifarwa:
Maleriya, kwalara, Tayipot, Amai, Gudawa, cutar ciwon sanyi da dai sauransu.
Ya kamata mu dage da tsaftace mahallimmu domin rashin tsafta gaskiya ba karamar illa bace kai za ma a iya kiran rashin tsafta ba karamar masifa bace, ban da cututtuka da yake haifarwa, rashin tsafta ya kan sa mutane su rika kyamarka, rashin tsafta har aure yake kashewa.
Hknyoyin magance wannan cutittika:
1.wanke hannu bayan an fito daga bayan gida, wanke hannu kafin a ci abinci sannan a yi Bisimillah.
2.Tsabtace ruwa kafin a yi amfani d shi a sha ko a yi girki
3. Wanke bandaki akai-aka domin gujewa cutittika
4. Rufe abinci da tsabtace shi.
5. Kwana da gidan sauro ko wajen da ba sauro
6. Gyara kwatoci domin gujewa taruwar sauro
7. Shara da wanke-wanke domin gujewa taruwar kananan cututtuka da ba’a ganinsu
8. Rufe abinci da abin sha domin kada kudaje masu yada cutar kwalara su shiga ciki.
Rukayya
Assalamu Alaikum Warahmatullah
Gaskiya rashin tsaftar cikin gida na haifar da kanana da manyan cututtuka, dalili kuwa shibne za ka ga mace ta fita gida tsaf amma cikin gidanta da kazanta ga wanke wanke ta barshi kuda ga wanki ta jika yana ta wari ga tsakar gidanta duk shara wanda hakan yana haifar da cututtuka irinsu kwalara da maleriya dadai sauransu don Allah mata mu gyara.
Daga Bilkisu Isma’il
Assalamu alaikum!
A gaskiya rashin tsafta cikin gida ba karamar cuta bane saboda yana haifar da cutittika da dama. Misali kamar maleriya, Tayipot, kwalara wato Amai da gudawa cutar ciwon sanyi na mata wanda wannan gaskiya ba karamar cuta bace, saboda idan cutar ta yi yawa har yana kai ga ya taba mahaifar mace, ki ga an zo ana ta wahala, wata ki ga ya zo ya kai ga har ana cewa ba za ta iya samun ciki ba saboda cutar ciwon sanyi ya ci karfinta ya kashe mata mahaifa.
Wani sai ki ga an je asibiti ana cewa sai am mata wankin mahaifa, sai ki ga wata idan Allah ya sa an dace shike nan ta samu lafiya, wata kuma a yi ta yi har ‘agaji a batta. To kin ga gaskiya duka wadannan cutittika da na lissafo ba kanana bane.
Ya kamata mata mu rage son jiki mu tashi mu gyara gidajan kullum kar mu bar gidajanmu da kazanta. Ita kazanta tana kawo tsana tsakaninki da maigida koda kuwa shi bashi da tsafta, duk namiji ba ya son kazamar mace sai ya ji duk ta fita a ransa , mata mu gyara.
Hanyoyin da za ki gyara ki zama mai tsafta: Za ki iya kasa aikin gidanki, tsari ne abin duk abin da kika yi amfani da shi kar ki bari wai sai kin zo shara a’a ki gyara wajen take sai ki ga gidanki ba zai na baci ba. Kuma kullum ki kasance kina shara, ki koyawa ‘ya’yanki.
Sannan kar ki zama mai tara wake-wake, saboda shima babbar kazanta ce wani abu zai iya zuwa ya yi ta lasa miki kwano baki sani ba.
Faddausi Dahiru
Assalamu alaikum!
Rashin tsafta cikin gida gaskiya yana haifar da cutittika da dama kuma ban ba cutittika wadanda za su iya kashe mutum ma idan ba a yi taka tsantsan ba, kamar su kwalara: kwalara tana iya kashe mutum idan ya zo da karar kwana ki ga mutum yana ta amai da gudawa, mutum ya kare ya lalace cikin kwana guda idan Allah ma ya sa zai samu lafiya kenan, amma ana wahala idan ta kama mutum.
Maleriya: Itama idan ta kama mutum, har ma idan ta ci karfin mutum ta wuce 1+, ana wahala za ki ga ba ta jin magani har sai an hada da allura.
Sai Tayipot shima idan ya kama mutum yana wahalar da shi. Abin da ke kawo shi rashin tsaftar ruwa, ko kasha ruwa marar kyau ko kuma abin da a ka zuba ruwan bashi da kyau dayan biyu ne.
Suna da yawa cutittikan, mata ya kamata mu daure, mu dage mu kuma jajirce wajen tsaftace muhallinmu, ke kanki idan kin tsaftar gidanki za ki ga kina jin dadin zama a ciki, sannan kuma iskar ma da za ta shigo za ki ji ta ta dabance mai dadi, babu wani wari.