Kwanan nan, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta samar da alkaluman yadda kasar Sin ta yi amfani da jarin waje a cikin rubu’in farko na bana, inda aka nuna cewa, a tsakanin lokacin, adadin sabbin kamfanoni masu jarin waje da aka kafa a kasar ya karu zuwa 12,603, wanda ya karu da kashi 4.3% idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar da ta gabata. Sai dai yawan jarin waje da aka yi amfani da shi a zahiri a kasar ya ragu da RMB biliyan 269 da miliyan 230, wanda ya ragu da kashi 10.8% bisa na makamancin lokacin bara.
Duk da cewa kudin jarin waje da aka yi amfani da shi a zahiri ya ragu, amma an samu sassaucin raguwar, idan aka kwatanta da lokacin watan Janairu da na Fabrairu, inda yawan raguwar ta sauka da kashi 9.6%. Abin lura kuma shi ne, a watan Maris, yawan jarin waje da aka yi amfani da shi a zahiri ya karu da kashi 13.2% bisa na makamancin lokacin bara.
- Zulum Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Boko Haram Ke Dawowa Wasu Yankuna A Borno
- An Gudanar Da Dandalin Kirkire-kirkire Na Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 4 A Birnin Qufu Na Kasar Sin
Bisa yanayin da duniya ke ciki na fuskantar rashin tabbas, samun sassaucin raguwar ya kasance wani abu mai wuyar gaske. Hakan ya kuma nuna yadda jarin kasashen waje ke bayyana kwarin gwiwa na dogon lokaci ga kasuwannin kasar Sin.
Alkaluman zuba jari na kasashen waje sun hau kan mizani mai kyau a rubu’i na farko, a kan hakan kuwa, kasar Sin za ta kara bude kofarta domin maraba da jarin waje na duniya. Har ila yau ana sa ran karin kamfanonin waje za su zuba jari da gudanar da kasuwanci a wannan kasa mai albarka.
Lokaci zai tabbatar da cewa, kasar Sin ta taba zama kyakkyawan wurin saka jari da ya dace, kuma tana kasancewa haka ma a yanzu, kana babu makawa a nan gaba za ta ci gaba da zama hakan ga ‘yan kasuwa na kasashen waje. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp