A wannan makon, muna tare da kwararriyar likitan nan; Dakta Maryam Ahmed Almustapha, wadda ta saba kawo mana gudunmawa a kan harkokin da suka shafi lafiyarmu; inda a wannan makon ta yi mana tsokaci a kan shangiya da illolinta.
Mutane da dama, na shan giya; duk da cewa sun san illarta, don jin dadi ko kawai da damuwa ko kuma samun nishadi a cikin jama’a.
- Kungiyar Masu Masana’antu Ta Samu Bashin Naira Biliyan 75 Daga Bankin BOI
- Jirgin Ruwan Aikin Jiyya Na “Peace Ark” Ya Kammala Aikinsa A Benin
A likitance a kiran giya da ‘Ethanol’, wadda ke zuwa kai tsaye cikin ciki ko hanji; daga nan kuma ta shiga cikin jini. Idan wannan giya ta shiga cikin jini, tana wucewa ne kai tsaye zuwa cikin hanta; don haka hata, ita ce ke da babban aiki a gabanta.
Matsalar da ake samu a nan ita ce, idan giyar ta je inda hanta take; da sauri take wucewa, don haka; hanta ba ta iya samun damar karkade dukkanin giyar da mutum ya sha a lokaci guda; har sai jinin ya yi ta zagayawa kafin ta iya tace giyar.
Amma inda matsalar take, kafin jinin ya kammala zagayawa hantar, sai ya bi ta kwakwalwa tukunna; kuma a wajen giyar take yin aiki.
Kwakwalwarmu na da kwayoyin halittar da ke kula tare da iya rike abubuwa da kuma tunawa da su, sannan kuma; kwakwalwar na da wata kwayar halitta da ke taimakawa wajen kwantar wa da mutum hankali.
Saboda haka, idan giya ta shiga kwakwalwar mutum; tana zuwa ne ta kara aikin kwayoyin halittar da ke kulawa wajen rike abubuwa tare kuma da rage aikin kwayar halittar da za ta kwantar wa da mutum hankali.
Har ila yau, a kwakwalwarmu akwai bangarori daban-daban, akwai bangaren da idan giyar ta je; tana sa wa mutum ya manta abubuwa ko ya kasa yin magana ko kuma yin tunani mai kyau.
Akwai kuma, wajen da idan giyar ta je a kwakwalwa; za ta hana mutum tafiya yadda ya kamata ko hana shi yin tunani mai kyau; inda zai kasance yana yin abubuwa tamkar karamin yaro.
Babbar inda matsalar take, da zarar mutum ya yi sabo da shan giya; da zarar bai sha ba, ba zai taba jin dadi ba. Sannan, da zarar mutum ya raya a ransa cewa, yana so ya sha giyar; ba zai taba samun nutsuwa ba, har sai ya sha; domin kuwa mutum zai rika jin damuwa; ya kasa zama wuri guda, har ma ya kasa yin barci.
Haka nan, giya na sa ruwan jikin mutum ya rika saurin konewa; dole mutum ya rika yawan shan ruwa. Sannan, giyar tana sa fuskar mutum ta yi ja ko yawan samun ciwon kai da amai. A takaice dai, giya na matukar illata hanta tare da karfafa ciwon Olsa ga masu ita.
Bugu da kari, giya na kara ta’azzara ciwo ga masu hawan jini da masu fama da ciwon Siga tare kuma da barazanar kara ciwon zuciya da bugawarta. Don haka, a shawarce dai; a sha ruwa, amma kada a sha giya.