Sanin kowa cewa, shan taba ba karamin al’amari ba ne; musamman wajen cutar da lafiyar Dan Adam, wannan dalili ne ya sa a kowane lokaci likitoci ke ci gaba da wayar da kan mutane, domin kaurace wa shan nata.
A wannan mako, za mu yi tsokaci ne a kan illar da ta’ammali da shan tabar ke yi wa mata, musamman masu dauke da juna biyu. Wadannan illoli na da dama, amma za mu yi kokarin fito da wasu daga cikinsu, domin wadanda ba su sani ba; su sani.
- Darussa Daga Rayuwar Shehu Ibrahim Inyass (RA) Wajen Yada Musulunci (II)
- Gidauniyar M-TECH Ta Tallafawa Yara Mabukata 400 Da Tallafin Karatu A Jihar Kebbi
Mafi yawan lokuta, maza ne ke koya wa matayensu wannan dabi’a ta shan taba ko kuma idan sun zuki tabar su rika fesa musu hayakin. Don haka, ga dai irin illar da shan tabar ko fesa musu hayakin ke haifar musu:
Da farko dai, yana iya hana mace daukar ciki kwata-kwata ko kuma idan ta samu cikin ta yi barin sa.
Kazalika, idan macen har ta iya daukar cikin; da zarar ta tashi haihuwa akwai yiwuwar jaririn nata ya kasance dan kankani, wanda kamar yadda aka sani; haihuwar kankanin jariri nan gaba ka iya haifar masa da cututtuka kamar na ciwon siga, ciwon zuciya ko ya kasance mai dan karamin kai, wanda ka iya sa wa ya kasance mai matsalar kwakwalwa.
Haka zalika, wannan dalili na iya sa wa jaririn ya kamu da ciwon da ake kira ‘infection’ na hunhu ko zuciya ko kunne ko kuma na kwakwalwa.
Saboda haka, mace ta sha taba ko shinsha ko kuma a rika busa mata hayakin tabar, babbar matsala ce, don haka ya kyautu maza su kiyaye wannan kwarai da gaske.