Shugaban Hukumar Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya koma bakin aiki a hukumar bayan sulhu da aka yi masa da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.
Sheikh Daurawa ya koma bakin aikinsa a ranar Talata a hedkwatar hukumar da ke unguwar Sharada.
- An Dauki Nauyin Karatun Matuƙin Adaidaita Sahun Da Ya Tsinci Miliyan 15 A Kano
- An Sulhunta Gwamnan Kano Da Sheikh Aminu Daurawa
A daren ranar Litinin ne wata tawagar zauren malaman jihar, ta jagoranci yin sulhu tsakanin gwamnan jihar da malamin.
Tun da fari dai Sheikh Daurawa, ya yi murabus daga shugabancin Hisbah bayan da Gwamna Abba ya soki yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta.
Kalaman gwamnan sun bar baya da kura, inda suka haifar da cece-kuce a jihar, lamarin da ya kai ga wasu fara janye mubaya’arsu ga gwamnatin jihar.
Sai dai tun bayan faruwar lamarin, gwamnatin jihar ta kafa kwamiti na musamman domin dannar kirjin malamin tare da rokonsa ya dawo kujerarsa.
A lokacin dai kafafen sada zumunta sun dauki dumi kan lamarin, inda kowa ke bayyana ra’ayinsa game da kalaman gwamnan da kuma murabus din Sheikh Daurawa.
Bayan yin sulhu a tsakanin Sheikh Daurawa da gwamnan jihar, malamin ya fitar da sabuwar sanarwa na bai wa masu baÉ—ala a jihar wa’adin mako biyu su tuba ko kuma su bar Jihar Kano.
A gefe guda kuma, Gwamna Abba ya yi alkawarin gyara wasu gine-gine da sabunta kayan aiki a hukumar Hisbah don ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.