Shugabanni sun yi kira ga ‘yan Nijeriya musamman Musulmi da su rungumi darussa muhimmanci Maulidin haihuwar Annabi Muhammad da dabi’unsa da a wannan kakar bana.
Shugabannin sun kuma karfafa gwiwar ‘yan Nijeriya da bar wannan gagarumin biki ya zama abin koyi ga dabi’un Ma’aiki na soyayya, tausayi, da hakuri da juna, wadanda ke da matukar muhimmanci ga rayuwa a Nijeriya.
- Kwangilar Biliyan 30: PDP Ta Bukaci EFCC Ta Binciki Gwamnatin Sakkwato
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 4 A Birnin Gwari Da Giwa Bayan KuÉ“utar Da Mutane 20Â
A ranar Lahadi ce Musulman Nijeriya suka bi sahun Musulman duniya wajen yin murna da zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW).
Shugabanni a Nijeriya sun taya al’ummar Musulman murnar Maulidi, Shugaban kasa Bola Tinubu da daukacin gwamnonin Nijeriya suka aike da sakon taya murna tare da taya al’ummar Musulmi murna bisa zagayowar Maulidin wannan shekara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce shugaban kasa Tinubu ya bukaci Musulmai da su yi amfani da wannan lokaci domin kyawawan halaye da koyarwar Manzon Allah.
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rika zurfafa game da rayuwar Annabi Muhammad, tare da bayyana kyawawan halaye kamar zaman lafiya, hakuri da juriya a yayin gudanar da bukukuwan Mauludi.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar, gwamnan ya bukaci mabiya addinin Islama da su ci gaba da zaman lafiya, yana mai cewa Annabi Muhammad ya yi rayuwar da ta dace a yi koyi da ita a wannan lokaci.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya nuna damuwarsa kan halin kuncin da tattalin arzikin kasar ke ciki wanda ya sanya rayuwa cikin wahala ga daukacin ‘yan Nijeriya.
A cikin sakon fatan alheri na bikin Maulidin bana, wanda mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Kwamared Mukhtar Gidado ya fitar a ranar Lahadi, gwamnan ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan bala’i.
Gwamnan Jihar Filato Barr. Caleb Mutfwang ya mika sakon taya murna ga al’ummar musulmin jihar da ma sauran jihohin kasar nan na murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad.
A cikin wata sanarwar manema labarai da daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Gyang Bere ya fitar, ya ce gwamnan ya jaddada mahimmacin Maulidi ga al’ummar Musulmi.
Shi ma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Wike ya tunatar da mazauna garin Abuja cewa ranar ba wai kawai ta kasance a matsayin biki ba ce, ta kasance koyi da kyawawan halaye da dabi’u da koyarwar Annabin da ke da tausayi da tawali’u da adalci.
Baya ga gwamnatin tarayya ta bayar da hotu a ranar Litinin 16 ga watan Satumba, bisa gimama mihimmancin wannan rana, yayin da gwamnatin Jihar Jigawa ta kuma ayyana ranar Talata 17 ga watan Satumba 2024 a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar Mauludin Annabi Muhammad (S.A.W).