A ’yan shekarun baya bayan nan, hankulan duniya na kara karkata ga zakulo dabarun dakile kalubalen sauyin yanayi, karkashin hadin gwiwar dukkanin sassan kasa da kasa.
Kuma a bana, yunkurin kasashen duniya a wannan fanni ya karfafa, sakamakon taron COP27 na bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD da aka gudanar a baya bayan nan a kasar Masar, wanda ya kasance babban dandali ga daukacin masu ruwa da tsaki, na hada karfi da karfe wajen lalubo dabarun gaggawa na shawo kan kalubalen sauyin yanayi.
- Zaben 2023: Majalisar Dinkin Duniya Da ECOWAS Sun Yi Sabon Gargadi
- Ban Taba Jin Kunyar Sana’ar Sayar Da Maganin Mata Ba -Sahura Haruna
Ma’anar sauyin yanayi
Sauyin yanayi na nufin sauyi mai tsawo na zafi, da sauran abubuwa masu alaka da jirkitawar yanayin muhalli na ainihi. Wannan sauyi na iya zama mataki da zai auku ba tare da sa hannun bil adama ba. Sai dai tun daga shekarun 1800, ayyukan yau da kullum na dan adam sun zamo a sahun gaba wajen ingiza sauyin yanayi, musamman ta hanyar kona albarkatun mai da kwal, wadanda dukkanin suke fitar da nau’o’in iska mai dumama yanayi da sauya yanayin duniya na asali. Masana na cewa, bangaren kona albarkatun mai shi ne kan gaba da kaso mafi rinyaje cikin abubuwan dake haifar da sauyin yanayi, domin kuwa ta karkashin wannan fanni ake fitar da kaso sama da 75 bisa dari na nau’o’in iska mai dumama yanayi, da ma kusan kaso 90 bisa dari na iskar “carbon dioxide”.
Masana na cewa nau’o’in iska masu dumama yanayi na lallube duniyar bil adama, tare da kange zafin rana daga ficewa daga doron duniya.
Dalilan dake haifar da sauyin yanayi
Masana da masu bincike sun tabbatar da cewa, muhimman dalilan dake haifar da sauyin yanayi sun hada da ayyukan sarrafa makamashi domin samar da lantarki, da kona albarkatun mai a masana’antu, da gidaje da ababen hawa.
Har ila yau, akwai batun sare dazuzzuka, inda alkaluma suka nuna cewa, a duk shekara bisa kiyasi, ana sare fadin daji da ya kai hekta miliyan 12.
Kuma da yake dazuzzuka na zuke iskar “carbon dioxide” mai dumama yanayi, sare dazuzzukan na mayar da hannun agogo baya, a yunkurin da ake yi na magance wannan kalubale.
Masana sun ce sare dazuzzuka, tare da ayyukan noma, da sauran ayyukan da bil adama ke yi domin amfanin yau da kullum, su ne ke haifar da kaso daya bisa hudu na nau’o’in iska mai dumama yanayi dake addabar duniya.
A daya bangaren kuwa, masana na cewa, ko shakka babu idan har bil adama na son ganin bayan tasirin sauyin yanayi, wajibi ne ya mayar da hankali ga dakile dumamar yanayi ta hanyar bunkasa samar da makamashi daga karfin iska, da hasken rana, da sauran nau’o’in makamashi da ake iya sabunta amfani da su.
An dai yi ittifaki cewa, ya zama dole dukkanin sassan duniya su yi hadin gwiwa da juna, wajen gano dabarun rage radadin sauyin yanayin, da gano fasahohin kimiyya, da na zamantakewa, wadanda za su baiwa dan adam damar jurewa, da dorewar rayuwa tare da kalubale masu nasaba da sauyin yanayi, da lalubo dabarun rage asarar da sauyin yanayin ka iya haifarwa ga al’ummun duniya a nan gaba, da ma batun samar da kudaden gudanar da wadannan ayyuka.
Kaza lika an yi amannar cewa, nahiyar Afirka da sauran sassan kasashe masu tasowa, na cikin yankunan duniya dake fitar da mafi karancin sinadarai, da nau’o’in iska mai gurbata, ko dumama yanayin muhallin duniya, amma a hannu guda, nahiyar da ma wasu kasashe marasa sukuni, su ne a sahun gaba wajen dandana kuda daga mummunan tasirin sauyin yanayi.
Alkaluma sun nuna cewa, kasashen masu ci gaban masana’antu da suka hada da Sin, da Amurka, da Indiya, da Rasha, da Japan, da Jamus, da Iran, su ne kan gaba wajen fitar da sinadarai, da nau’o’in iska mai gurbata, ko dumama yanayin muhallin duniya.
A bana, sassan Turai sun fuskanci karuwar zafi mafi muni a tarihi, da gobarar daji, kana kasashen Najeriya da Nijar da Pakistan sun fuskanci ambaliyar ruwa da aka jima ba a ga irinta ba, wasu sassan duniya kuwa sun fuskanci karuwar mahaukaciyar guguwa mai hade da tumbatsar teku da ambaliya. Buga da kari, kasashen Kenya da Habasha a gabashin Afirka, na ci gaba da fuskantar fari mafi muni cikin shekaru masu yawa.
A cewar shirin abinci da aikin gona na MDD ko WFP, adadin mutane daga yankin kahon Afirka dake fama da karancin abinci, ya karu daga mutum miliyan 135 a shekarar 2019 zuwa mutum miliyan 345 a yanzu.
Wannan wani bangare ne kawai, na jimillar al’ummun duniya da yawansu ya kai miliyan 50 daga kasashe 45 dake fuskantar barazanar fadawa yanayi na fari.
A jimlace, sauyin yanayi na haifar da kamfar ruwa a sassan duniya daban daban, yana haifar da karuwar zafi, da fari wanda ke shafar yawan yabanyar da ake iya samu daga ayyukan noma, da lalacewar muhallin halittu, da kwararar hamada.
Kazalika sauyin yanayi na haifar da karuwar barazanar ambaliyar teku, da bacewar wasu nau’o’in tsirrai da halittu, da kamfar cimaka tsakanin al’ummun duniya.
Bugu da kari, sauyin yanayi na haifar da barazanar barkewar cututtuka masu nasaba da gurbacewar iskar shaka.
A duk shekara, yanayin sauyawar muhalli na sabbaba rasuwar mutane kusan miliyan 13 a sassa daban daban na duniya.
Haka kuma, sauyawar salon yanayin muhalli yana ingiza bazuwar cututtuka, irin wadanda ke fin karfin tsarin kiwon lafiya da bil Adama ke da shi.
A daya hannu kuma, mutane da dama na kauracewa muhallansu sakamakon matsalolin dake tattare da tasirin sauyin yanayi, ta yadda hakan ke shafar lafiyar kwakwalwa, da gurguncewar tattalin arzikinsu.
Da yake kasashe masu sukuni ne kan gaba wajen gudanar da ayyuka dake haifar da gurbatar yanayi, an yi ta gudanar da taruka na kasa da kasa da nufin tattaunawa wannan matsala, tare da yin kiraye-kiraye na samar da kudaden diyya ga kasashe masu tasowa da matalauta, ta yadda za su samu damar rage radadin wannan matsala.
Bayan tattaunawa da gudanar da shawarwari masu yawa, kasashen duniya sun kaddamar da taron shekara-shekara game da sauyin yanayi, karkashin yarjejeniyar yanayi ta MDD, wadda aka amince da ita a shekarar 1992.
Karkashin wannan yarjejeniya ne kuma gwamnatocin kasashe daban daban, suka amince da aiwatar da manufofi na takaita karuwar ma’au’in zafi, da matakan dakile munanan tasirin sauyin yanayi.
Kazalika karkashin dandalin kasashen da suka amince da wannan yarjejeniya, an kafa asusun musamman na tallafawa sassan da suke tafka asara sakamakon tasirin sauyin yanayi.
Duk da cewa asusun bai yi tasirin da ya kamata ba, sakamakon gaza cika alkawuran samar da kudaden aiwatar da shi, a hannu guda, ya zamo tamkar sanya dan-ba ga ayyukan da suka biyo baya a fannin.
Tsakanin ranakun 6 zuwa 20 ga watan Nuwamban bana, an kira taro na 27, na kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD ko UNFCCC a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar.
Kuma gabanin kammalarsa, kasashe mahalarta sun amince da kafa sabon asusun musamman, wanda zai tattara kudaden tallafawa kasashen dake fuskantar barazanar sauyin yanayi, ta yadda za su iya tunkarar ayyukan yaki da tasirinsa yadda ya kamata.
An cimma matsayar cewa, asusun zai samar da kudaden diyyar asara, da lalacewar muhalli, da fatan asusun zai yi aiki yadda ya kamata.
Har ma babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya ce taron na bana, ya zamo wani ginshiki mai muhimmanci na tabbatar da adalci.
Ya ce duk da cewa kudaden da ake fatan tarawa ba za su isa ba, tara kudin tamkar tabbatar da aniyar siyasa ce da za ta sake gina amincin da ya riga ya gurgunce tsakanin sassan kasa da kasa kan batun sauyin yanayi.
Ko shakka babu a taron COP27 na bana, kasashe masu wadata sun fito da muhimman batutuwa da suka dace, kamar batun samar da kudade, da tallafin kwarewa da kasashe masu tasowa ka iya cin gajiyar su, tare da fatan kasashe masu wadata za su yi aiki tare da sauran sassan kasa da kasa, wajen gina yanayi mai dorewa domin gaba.
Shirin kasar Sin na kafa tarihin nasara a fannin yaki da sauyin yanayi
Kasar Sin babbar kasa ta biyu a karfin tattalin arziki, kuma kasa mai tasowa mafi girma a duniya, don haka fannoninta na ayyukan masana’antu da sarrafa hajoji na kan gaba a duniya.
Dalilin hakan ya sa ta zama cikin manyan kasashen duniya masu sukuni, dake fitar da tarin nau’o’in sinadarai da iska mai dumama yanayi.
Sai dai sabani wasu kasashe dake kokarin kawar da kai, ko gaza cika alkawura game da magance sauyin yanayi, Sin ta yi rawar gani wajen sauke nauyin dake wuyanta, a fannin rage fitar da wadannan nau’o’in iska, da ma sanya wa’adin kaiwa ga yanayin daidaito tsakanin iskar Carbon mai dumama yanayi da take fitarwa da matakan kawar da ita.
A baya bayan nan ma, wakilin musamman na kasar Sin game da sauyin yanayi Xie Zhenhua, ya karfafa gwiwar kasashe masu sukuni, ta hanyar yin kira gare su da su ba da gudummawa, ga cimma nasarar manufofin dake kunshe cikin yarjejeniyar Paris, ta hanyar kafa asusun diyyar asara, da lalacewar muhalli karkashin yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD ko UNFCCC, domin taimakawa kasashe masu tasowa, ta yadda za su shawo kan kalubalen sauyin yanayi.
Masharhanta na ganin cewa, duba da yadda kasar Sin ke kan gaba wajen cin gajiya daga fasahohin dakile sauyin yanayi, musamman fannin bunkasa amfani da nau’o’in makamashi marasa gurbata muhalli, da wadanda ake iya sabuntawa. Kuma kasar ta jima da kasancewa abokiyar tafiya ga kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa a dukkanin fannonin ci gaba, yanzu lokaci ya yi da kasashe masu tasowa za su rungumi tafiya tare da Sin a wannan fanni.
A cewar Frederick Mutesa, wani kwararre a fannin ilimin samar da ci gaba dan kasar Zambia, kasar Sin ta nunawa duniya kwazonta a fili, wajen bunkasa ci gaba mai dorewa, da raya manufofi, na dakile kalubale, da matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa.
Ko shakka babu wannan shawara ce mai kyau, domin kuwa akasarin kasashen nahiyar Afirka da sauran sassan kasashe masu tasowa, na da albarkatu musamman na hasken rana, yayin da a daya bangaren kasar Sin ke da kwarewa, da fasahohin bunkasa samar da makamashi ta hasken rana, wanda hakan ke nuna cewa, idan har sassan biyu sun yi hadin gwiwa, tabbas za a ci babbar gajiya daga makamashi maras gurbata muhalli.
Baya ga fannin raba fasahohi da kasashen Afirka, fannin samar da kudaden dakile tasirin sauyin yanayi, shi ma muhimmin bangare ne da kasashen Afirka za su iya cin gajiya daga Sin, kasancewar dama akwai kyakkyawar dangantaka, da cudanya tsakanin kasashen Afirka da Sin karkashin dandalin FOCAC, na bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kuma irin tallafi na samar da manyan ababen more rayuwa da kasashen Afirka ke samu daga Sin, karkashin manufofin samar da ci gaba na shawarar “ziri daya da hanya daya”.
Tarihi ba zai manta da ci gaban da Sin ta cimma a fannin amfani da makamashi da ake iya sabuntawa ba, ta yadda kasar ta kafa wani misali na yadda ya kamata kasashe masu tasowa ya dace su yi yaki kafada-da-kafada da wannan kalubale na sauyin yanayi.
Karkashin manufofin Sin, kasar ta cimma manyan nasarori a fannin sarrafa makamashi da ake iya sabuntawa, inda alkaluma suka nuna yadda a shekarar 2021 kadai, kasar ta zuba jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 380 a fannin sarrafa makamashi mai tsafta, adadin da ya haura wanda sauran kasashen duniya suka zuba a fannin.
A bangaren kirkire-kirkire ma, Sin na sahun gaba, inda ta samar da sabbin fasahohin zamani na sarrafa makamashi, tun daga na samar da lantarki daga karfin ruwa, zuwa na amfani da hasken rana, da karfin iska zuwa nukiliya. Dukkanin wadannan sassa na cikin jimillar hanyoyin samar da makamashi a kasar Sin.
Kaza lika daga shekarar 2012 zuwa 2021, Sin ta samu matsakaiciyar karuwar tattalin arziki da ta kai kaso 6.6 bisa dari a duk shekara, da karuwar kaso 3 bisa dari na adadin makamashi da kasar ke amfani da shi.
Har ila yau, adadin iskar Carbon dioxide da ake fitarwa a kasar bisa ma’aunin tattalin arziki na GDP ya ragu da kaso 34.4 bisa dari, yayin da kasar ta yi nasarar rage kona makamashin Kwal da kaso mai yawa a tsakanin shekaru kusan 10.
Masu fashin baki na ganin cewa, akwai shaidu dake nuna yiwuwar dorewar hadin gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashe masu tasowa, musamman a fannonin sauya alkiblar sarrafawa, da amfani da makamashi daga nau’o’in albarkatun mai, zuwa makamashi masu tsafta, da wadanda ake iya sabunta amfani da su da ma na bola-jari.
Sai dai fa duk da hakan, akwai babban nauyi a wuyan sauran manyan kasashe masu arzikin masana’antu, wadanda ke samar da karin kaso mai tsoka na abubuwan dake dumama yanayi.
A shekarun baya bayan nan, kasar Sin na da tsare-tsare na dogon zango, dake da nufin dora kasar kan turbar karkata yanayin tafiyar da tattalin arzikinta, daga fannonin zuba jari kan ababen more rayuwa zuwa fannin kirkire kirkire, kana daga fannonin fitar da hajoji zuwa na kyautata kasuwannin cikin gida. Da wanzar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.
Fatan dai shi ne daukacin sassan duniya za su ci gaba da hada karfi da karfe, wajen tabbatar da nasarar manufofin da aka sa gaba, a fannin dalike mummunan tasirin sauyin yanayi, da wanzar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ta yadda dukkanin bil adama zai samu zarafin yin managartacciyar rayuwa a duniya.