Taron hadin gwiwa a kan harkokin tsaro na jihohi hudu da suka hada da Katsina, Sakwato, Kebbi, Zamfara da Maradi da ke jamhuriyyar Nijer, sun yanke shawarar hana shigowa da babur kirar Boder a kasar nan.
Taron ya amince da cewa hana shigowa da baburan da‘yan ta’adda ke amfani da su a jihohin guda biyar na tsawon shekaru biyu a wani mataki na rage ayyukan ta’addanci.
- Bukatar Samar Wa Kotunan Korafe-korafen Zabe Kudaden Gudanarwa
- Yara 3 Sun Tsere Daga Maboyar ‘Yan Bindiga Yayin Da Suke Barci A Abuja
Hakan na cikin abubuwan da taron na gwamnoni biyar wanda gwamnan Maradi, Sheibu Abubakar ya jagoranta kamar yadda yake kunshe a cikin takardar jawabin bayan taro wadda sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji MuntariLawal ya karanta.
Ya ce an tattauna kalubalen tsaron da jami’an tsaro ke fama da shi a lokacin da suke sauke nauyin da aka dora masu, hakan ya sa ya yi roko ga gwamnatin Nijeriya da kuma gwamnatin Jamhuriyar Nijer da su zuba karin kudade ga jami’an tsaro da ke aikin samar da tsaro.
Taron kuma ya karfafa gwiwa jihohin da abun ya shafa su taimaka wa jami’an tsaro da kayan aiki da suka hada da ababen hawa da kayan gyaransu domin ganin suna aiki a jihohi na kowane lokaci.
Taron ya kuma tattauna bukatar ganin ana saka jihohin Kaduna da Neja a cikin dukkan ayyukan kakkabe ‘yan ta’addada ake yi ta la’akari da suna da iyaka da jihohin da abun ya shafa.
Gwamnonin sun bayyana takaici duba da yadda ‘yan jarida ke bayyana ‘yan ta’addaa a matsayin jarumai a cikin rahotanninsu.
Don magance hakan gwamnonin sun shawarci hukumar kula da kafafen watsa labarun Nijeriya ta duba batun domin amfanin kasa.