Malaman addinin Musulunci sun gudanar da wani gagarumin taron hadin kai a tsakanin maz’habobi da darikun Musulunci a Makkah domin dinke baraka da rarrabuwar kai da ake samu a tsakaninsu.
Taron mai taken,“Gina gada tsakanin maz’habobin Musulunci da dariku”, ya samu halartar mabiya maz’habobi da darikun Musulunci daga ko ina a fadin duniya.
- Hajjin Bana: Karin Naira Miliyan 1.9 Ya Jefa Dubban Maniyyata Cikin Garari
- Mace Za Ta Iya Yin I’itikafi A Wannan Zamanin?
Kungiyar Kasashe Musulmi (MWL) ta shirya taron wanda Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz ya dauki nauyi. Malaman da suka halarci taron, sun bayyana aniyarsu ta inganta mu’amala domin farfado da gudunmawar da al’ummar Musulmi ke bayarwa wajen wayar da kan jama’a da samun ci gaba a duniya.
Shugaban kungiyar ta MWL, Mohammed Al-Issa, ya bayyana wani shiri da taron ya amince da shi na samar da daftarin da za a yi aiki da shi wajen tabbatar hadin kai a tsakanin maz’habobi da darikun Musulunci don tunkarar dimbin kalubalen da suka addabi Musulmi a duniya.
Haka kuma Al-Issa ya bayyana farin cikinsa da karbar bakuncin taron mai dimbin tarihi a Makkah tare da jaddada bukatar hadin kan al’ummar Musulmi.
Sai dai ya yi gargadi game da kalaman bangaranci, ya kuma yi kira da a rika yada labaran da suka dace a kafafen yada labarai da ke kara samar da hadin kai. Ya mika godiyarsa ga mahukuntan kasar Saudiyya kan goyon bayan da suke ba su tare da yin addu’ar Allah ya kara ba su nasara.
A jawabinsa, Babban Mufti na Saudiyya, Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh, wanda Dakta Fahd Al-Majid ya gabatar, ya jaddada muhimmancin hadin kan al’ummar Musulmi, tare da tsawatarwa kan illar rarrabuwar kawuna kana ya bayyana irin gudunmawar da malamai ke bayarwa wajen samar da hadin kai a tsakanin Musulmai.
Ya gode wa Babban Hadimin Masallatai Masu Alfarma Guda Biyu, Sarki Salman Bin Abdulaziz kan goyon bayan taron tare da yaba wa kokarin hadin kan musulmai karkashin jagorancin Yarima Mohammed Bin Salman kuma Firayim Ministan Saudiyya.
Shi kuwa a nashi bangaren, Babban sakataren Kungiyar Hadin kan Musulmi (OIC), Hissein Brahim Taha ya yaba wa Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bisa goyon bayan shirya taron. Ya tabbatar da cewa muhimmin taron zai inganta hadin kai a tsakanin maz’habobi da darikun Musulunci tare da shawarwarin da za a yi amfani da su wajen samar da hadin kai da magance sabani.
Taha ya kuma yaba wa kungiyar MWL bisa sadaukarwar da take yi wa Musulunci da Musulman duniya baki daya.
A gefe guda kuma, an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin kungiyoyin MWL da OIC kan hadin kai.
An rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Cibiyar Fikhu ta Musulunci ta MWL da Cibiyar Nazarin Fikhu ta kasa da kasa ta OIC domin bunkasa hadin gwiwa a fannin bincike.
Wasu malamai na ganin wannan taron zai cimma nasara, yayin da wasu ke ganin har yanzu da sauran rina a kaba.
Babban limamin masallacin rukunin gidaje na Lake Biew Phase 2 da ke Abuja, Malam Falalu Abdullahi ya bayyana cewa, tun lokacin da hukumomin Saudiyya suka dage dokar hana wadanda ba Musulmai shiga Harami ba suka sauka daga layi. Ya ce irin wannan taro ba zai samu nasara ba har sai mahukunta kasar sun dawo kan layi.
Yayin da shi kuwa, Malam Bello Abukakar ke da ra’ayin cewa lallai wannan taron zai samu nasara. Ya ce kiran mabiya maz’habobi da darikun Musulmi wurin guda da aka yi shi kansa babban nasara ce.
Ya kara da cewa yana da yakinin wannan taro zai samu nasarar hada kan al’ummar Musulmin duniya matukar kowane dan maz’haba zai amince da hadin kan Musulunci fiye da daukaka maz’haba ko darikar ko kungiyarsa.