BBC ta rawaito yadda ziyarar Malaman Nijeriya ta kasance a Jamhoriyar Nijar kan wani tayin da suka yi na neman taka irin tasu rawar a dambarwar da ta ɓarke tsakanin Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da kuma ECOWAS, Malaman addinin musulunci daga Nijeriya sun samu damar tattaunawa da shugabannin sojin Nijar.
Wani lamari na neman kaucewa zub da jini ya haɗe kan malaman Nijeriya da alokuta da dama suke yi wa juna kallon hadarin kaji.
- Hanyoyin Da Suka Kamata ECOWAS Ta Bi Wajen Warware Rikicin Nijar
- Yadda Malamai Suka Dirar Wa Batun Yaki Da Nijar
Ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaban kungiyar Izallah ta Nijeriya, malaman sun tattauna da sojojin juyin mulki na tsawon sa’o’i uku.
Sheik Bala Lau ya shaida cewa tun da fari sai da sojojin suka fara neman afuwa game da rashin sauraren tawagar tsohon shugaban Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi da sauransu.
“katse wutar lantarki da hana shiga da abinci Nijar ya janyo zanga-zanga kuma matasa sun fito a ranar, gudun kada a yi musu rashin ɗa’a in sojojin shi ya sa ba su iya ba su damar tattaunawa da su ba, amma sun ce mu bayar da haƙuri a madadinsu,” kamar yadda Bala Lau ya shaida.
Ta ɓangaren abin da suka cimma Malamain ya ce an samu ƙofar tattaunawar diflomasiyya, domin kuwa sojojin sun ce yanzu a shirye suke su tattauna da wakilan ECOWAS, a ko da yaushe.
“Tun daga yadda suka karɓe mu muka san cewa tafiyarmu ta yi nasara. Sun turo ministoci da Firaiministan ƙasar filin jirgin sama domin su zo su tare mu, sun kai mu kuma har fadar shugaban ƙasa da kansu.
“Mun tattauna kusan sa’a uku da su, mun tattauna kan abubuwa da dama. Mun isar da saƙo kuma mun yi nasiha domin a kiyaye zubar da jini, domin rikici idan an san farkonsa ba a san ƙarshensa ba.
“Mun ƙara nuna musu muhimmancin haɗin kai da ke tsakanin Nijeriya da Nijar, domin tarihi ne mai nisa,” in ji Sheik Bala Lau.
Ya ƙara da cewa sojojin NIjar sun yi farin ciki tare da murnar wannan ƙoƙari sun kuma nuna za su bayar da haɗin ƙai domin a samu a tattauna.
Bala Lau ya ce akwai wasu saƙonni masu yawa da za su isar ga Shugaban Najeriya da ECOWAS Bola Ahmed Tinubu waɗanda ba za su faɗu ba a waya.
Ko da aka tambaye shi game da lokacin da sojojin ke ganin ya dace a tattauna da su sai ya ce ” a ko ina aka kira su za su je kuma ko da yaushe”.
Cikin tawagar malaman akwai Sheik Bala Lau wanda ya jagoranci tawagar ya kuma gabatar da bayani.
Akwai Sheik Ƙaribullahi Nasiru Kabara da Sheik Ibrahim Dahiru Bauchi da Farfesa Khalid Sakataren ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam da Farfesa Salisu Shehu da dai suransu.