Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta jaddada cikakken goyon bayanta na samar da ƴan sandan jihohi a wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalar rashin tsaro a yankin da ma faɗin ƙasar baki ɗaya. Wannan tabbaci ya zo ne bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sabunta ƙudirinsa na tabbatar da samar da rundunar ƴan sandan jihohi.
Isma’ila Uba Misilli, babban daraktan hulɗa da manema labarai na Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa tuni gwamnonin suka ɗauki matsaya kan wannan al’amari. A cewarsa, kafa ƴan sandan jihohi na daga cikin matakan sake fasalin tsarin tsaro na Nijeriya domin magance matsalolin da suka addabi al’umma.
- Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi
- Ganawata Da Macron Ta Yi Amfani – Tinubu
Ƙungiyoyin al’adun gargajiya guda uku na Arewa da Kudancin Nijeriya sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta ɗaukar matakan da suka dace wajen samar da rundunar. Babbar ƙungiyar Arewa, wato Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta ce wajibi ne samar da ƴan sandan jihohi ya bi dukkannin sharuddan da kundin tsarin mulki ya tanada, tare da gargadin cewa kada gwamnonin su yi amfani da su wajen yaƙi da abokan adawa.
Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na ACF, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, ya bayyana cewa har yanzu ƙungiyar ba ta ɗauki matsaya a hukumance ba, amma wajibi ne a bi dukkan matakan da doka ta shimfiɗa. Ya nuna damuwa kan yiwuwar amfani da rundunar wajen muzgunawa abokan adawa da masu suka.
A nasa ɓangaren, tsohon Sanata daga Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa masu rajin kafa ƴan sandan jihohi dole ne su fahimci ƙalubalen da ke gaba. A cewarsa, “Waɗanda suke so tare da fatan ganin an kafa ƴan sandan jihohi, suke kuma sukar ƴan sandan tarayya, ina yi muku fatan abin da kuke yi wa kanku fata. Yayin da shugaban ƙasa a ƙarshe ya amince da ƴan sandan jihohi, za ku gane banbanci tsakanin rundunar tarayya da ta jihohi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp