Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPT) ta yi karin haske kan hukuncinta na tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin shugaban kasa.
Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi zargin cewa, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta tafka kura-kurai a yayin gudanar da zaben shugaban kasa da aka gudanar a 25 ga watan Fabrairu.
Don gane da cewa, ko Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta yi daidai wajen cewa, Tinubu na jam’iyyar APC shi aka zaba da kuri’u masu rinjaye, Kotun ta ce mai shigar da kara – PDP da dan takarar, Atiku Abubakar – ba su yi nasarar tabbatar da zarge-zargen da suka yi ba.
Mai shari’a Haruna Tsammani, shugaban kwamitin alkalai biyar, ya ce, “Don haka wannan zarge-zargen da aka yi kan Jam’iyyar APC da dan takararta, bai dace ba. Ina tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa na tarayyar Nijeriya.”