• English
  • Business News
Tuesday, August 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Tsoffin Abokai Ke Kafa Sabuwar Makoma A Tsakaninsu

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Yadda Tsoffin Abokai Ke Kafa Sabuwar Makoma A Tsakaninsu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

“Shugabannin kasashen Sin da Brazil sun kafa tarihi.”, “Ziyarar da shugaban kasar Brazil Lula ya kawo kasar Sin, ta bude kofa ga kasar ta Brazil.” kuma “Bayan ganawarsa da shugaban kasar Sin Xi Jinping, jakar shugaba Lula ta cike da yarjejeniyoyi da ma tsare-tsaren hadin gwiwa daban-daban.”

Ziyarar shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva a kasar Sin wanda ya kammala jiya Asabar 15 ga watan Afrilu, ta samu jawabai masu kyau daga kafofin yada labarai na kasar Brazil da sauran sassan kasar. An kuma yi imanin cewa, shugabannin kasashen biyu sun tsara hanyar da za a bi a mataki na gaba na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, tare da samar da sabuwar kyakkyawar makoma ga hadin gwiwar kasashen biyu.

  • Kasar Sin Ta Harba Wani Sabon Tauraron Dan Adam Dake Nazarin Yanayi

A bana ne ake cika shekaru 30 da kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Brazil, kuma shekara mai zuwa za a cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya, kuma a wannan muhimmin lokaci, ziyarar da shugaba Lula ya kawo kasar Sin daga ran 12 zuwa 15 ga watan Afrilu, ta jawo hankalin jama’a matuka.

Bisa sakamakon shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kuma sanarwar hadin gwiwa da bangarorin biyu suka fitar, ziyarar Lula a kasar Sin ta samu cikakkiyar nasara. Shugaba Lula na kasar Brazil ya bayyana cewa, babban burin ‘yan majalisar dokokin kasarsa da dukkan bangarorin al’umma shi ne karfafa dangantakar da ke tsakanin kasar Brazil da kasar Sin a dukkan matakai.

Zaman lafiya da ci gaba da kuma zamanantar da kasar, su ne manyan burikan al’ummomin kasashen biyu wato Sin da Brazil. An yi imanin cewa, bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Brazil a sabon zamani, za ta bunkasa zuwa sabon matsayi, wanda zai kawo karin alheri ga jama’ar kasashen biyu da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da yankin Latin Amurka da ma zaman lafiya da ci gaban duk duniya.(Ibrahim)

Labarai Masu Nasaba

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 26

Next Post

Ngozi Okonjo-Iweala: Sin Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Inganta Tsarin Ciniki A Tsakanin Bangarori Daban-Daban

Related

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing
Daga Birnin Sin

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

12 hours ago
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO
Daga Birnin Sin

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

12 hours ago
CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II
Daga Birnin Sin

CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

13 hours ago
Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” a Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO
Daga Birnin Sin

Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” a Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO

15 hours ago
Wani Rahoton Kasar Sin Ya Kalubalanci Halaccin Ayyukan Amurka Bisa Dogaro Da “’Yancin Zirga-zirga”
Daga Birnin Sin

Wani Rahoton Kasar Sin Ya Kalubalanci Halaccin Ayyukan Amurka Bisa Dogaro Da “’Yancin Zirga-zirga”

16 hours ago
Beijing Zai Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani A Wuraren Adana Kayan Tarihi
Daga Birnin Sin

Beijing Zai Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani A Wuraren Adana Kayan Tarihi

18 hours ago
Next Post
Ngozi Okonjo-Iweala: Sin Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Inganta Tsarin Ciniki A Tsakanin Bangarori Daban-Daban

Ngozi Okonjo-Iweala: Sin Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Inganta Tsarin Ciniki A Tsakanin Bangarori Daban-Daban

LABARAI MASU NASABA

Mutane Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

Mutane Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

August 26, 2025
Ɗaruruwan ‘Yan APC Sun Koma ADC A Sakkwato Saboda Rashin Tsaro Da Talauci

Ɗaruruwan ‘Yan APC Sun Koma ADC A Sakkwato Saboda Rashin Tsaro Da Talauci

August 26, 2025
Yajin Aikin ASUU Na Barazana Ga Ci Gaban Kasa

ASUU Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Rashin Cika Mata Alƙawura

August 26, 2025
Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

August 26, 2025
Ɗan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya

Ɗan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya

August 26, 2025
Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

August 26, 2025
An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

August 25, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

August 25, 2025
CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

August 25, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gargadin Jihohin Arewa 9 Kan Afkuwar Ambaliya 

August 25, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.