Biyo bayan samun rahoton mutuwar mutum 29 a wani turmutsutsu guda biyu a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma Jihar Anambra, Rundunar ‘yansanda ta fitar da tsauraran ka’idoji ga masu shirya rabon kayan abinci don kaucewa afkuwar lamarin nan gaba.
A Jihar Anambra, wanda ya auku a Okija da ke Karamar Hukumar Ihiala, an sanar da mutuwar mutum 19, yayin da wasu 32 suka samu raunuka daban-daban.
- Muhammad Bashir Ya Zama Sakataren Yaɗa Labaran Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban AKCILS
- Amurka Da Phillippines Sun Hada Karfi Don Kalubalantar Sin Kan Batun Tekun Kudancinta
Turmutsutsun ya afku ne a lokacin da wani mai raba tallafin abinci, Cif Ernest Obiejesi, wanda aka fi sani da Obi Jackson, ke raba shinkafar Kirsimeti kyauta a gidansa na Okija.
A wani turmutsitsin da aka yi a Abuja, an ce mutum 10 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a cocin Holy Trinity Catholic da ke Maitama da safiyar Lahadin da ta gabata.
Mummunan lamarin ya faru ne a yayin wani aikin rabon kayan tallafi da cocin ta shirya domin samar da agaji ga talakawa mazauna yankunan da ke kusa da su ciki har da kauyukan Mpape da Gishiri.
Tinubu ya soke duk wani taron da zai gabatar a Jihar Legas domin karrama wadanda abin ya shafa
A wani mataki da ya dauka kan faruwar lamarin, Shugaba Bola Tinubu ya soke duk wani taron da zai gabatar a Legas jiya, ciki har da halartar bikin Regatta na Legas na 2024, don karrama wadanda abin ya shafa.
A cewar wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasar, Bayo Onanuga ya fitar, an shirya shugaban zai kalli faretin jirgin ruwa da sauran ayyukan jiragen ruwan Regatta daga bakin ruwa na titin Kueen’s Dribe.
Manyan baki da suka hada da manyan jami’an gwamnatin Jihar Legas da masu rike da sarautun gargajiya na jihar sun riga sun zauna a lokacin da Shugaban ya soke zuwansa bayan bayyanar faruwar bala’in.
Da yake jajantawa wadanda abin ya shafa na Anambra da na Babban Birnin Tarayya, Tinubu ya bukaci jihohi da hukumomin da abin ya shafa da su aiwatar da tsauraran matakan dakile taron jama’a cikin gaggawa.
Ya kara da cewa abin takaici ne matuka yadda abubuwan da suka faru a cocin Holy Trinity Catholic da ke Maitama a Abuja da kuma wata cibiyar al’umma da ke Okija a Jihar Anambra, suna da kamanceceniya da abin da ya faru a garin Ibadan na Jihar Oyo.
Yayin da yake addu’ar Allah ya jikan ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda suka mutu a turmutsutsun, ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Ya sake nanata cewa ana iya guje wa wadannan barna idan masu tsara taron sun bi ka’idojin kiyayewa da ka’idojin da suka dace don tabbatar da tsaro kafin da kuma bayan taron.
“A cikin lokacin farin ciki da murna, muna bakin ciki tare da ‘yan kasa suna jimamin radadin da ‘yan uwansu suke yi. Addu’o’inmu na ta’aziyya da waraka suna tare da su,” in ji Shugaba Tinubu.
Saboda haka, ‘yansanda sun ce masu shirya irin wannan ayyukan agaji dole ne su sanar da ‘yansanda kafin abubuwan da suka faru don tabbatar da kula da jama’a yadda ya kamata.
Shi ma a nasa martanin, babban sufeton ‘yansandan kasar, IGP Kayode Egbetokun, ya yi gargadin a guji raba kayan abinci ba tare da nuna bambanci ba yayin da ake fara bukukuwan Kirsimeti.
IGP ya yi tambaya kan yadda ba a shirya rabon kayayyakin jin kai da na agaji a kasar nan ba a lokacin bukukuwan.
PRO, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya shaida wa manema labarai a wajen taron cewa, gargadin ya biyo bayan wasu munanan al’amura da ke nuna bukatar da ake da ita ta samar da tsari mai inganci wajen isar da kayan agaji ga al’ummomi masu rauni da kuma jama’a baki daya.
PRO ya ce, “Bisa la’akari da wannan ci gaba, IGP ya yi kira ga jami’an gwamnati, shugabannin al’umma, da kungiyoyi masu zaman kansu da su yi aiki tare don samar da cikakken tsari na raraba kayan agaji.
“Shugaban rundunar ‘yan sandan ya gargadi kungiyoyi da masu shirya irin wannan lamari da su tabbatar da shigar jami’an tsaro hannu domin sakaci a bangarensu laifi ne kuma ba za a manta da su ba, kamar yadda sashe na 196 na kundin laifuffuka da sashe na 344 na kundin laifuffuka suka tanada. Dokokin Tarayyar Nijeriya.”
Ya ce IGP din ya kuma karfafa wa jama’a da za su amfana da irin wannan rabon, da su yi taka-tsantsan tare da ba da fifiko wajen kare lafiyarsu domin gujewa bala’in da ba a zata ba.
IGP din ya kuma umarci kwamishinonin ‘yansandan jihohin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike kan wadannan munanan al’amura domin ci gaba da shari’a.
Har ila yau, rundunar ‘yansandan FCT, yayin da ta ke nuna rashin jin dadin ta game da lamarin, ta yi kira da a bi shawarwarin tsaro da tsare-tsare game da irin wannan lamari, gami da sanar da ‘yansanda tun da wuri.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan, SP Josephine Adeh ta sanya wa hannu, hukumar ‘yansandan ta ce turmutsitsin da ya yi sanadin mutuwar mutum 10 da suka hada da yara hudu da kuma jikkata wasu takwas ya faru ne da misalin karfe 6:30 na safe.
Ya ce hudu daga cikin wadanda suka jikkata an yi jinyarsu kuma an sallame su, yayin da sauran wadanda suka jikkata ke ci gaba da samun kulawa a asibi. Rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma rundunar hadin gwiwa ta FCT sun kwashe sauran jama’a sama da dubu daya.
“A cewarsa, kwamishinan ‘yansanda CP Olatunji Disu, ya ziyarci wadanda abin ya shafa a asibiti domin bayar da taimako da kuma kwantar da hankula.
Ya ci gaba da cewa: “Don hana faruwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba, rundunar ta ba da umarnin cewa duk kungiyoyin addini, ko daidaikun mutane da ke shirya taron jama’a, ayyukan agaji ko manyan taruka a Babban Birnin Tarayya, dole ne su sanar da rundunar ‘yansanda tukuna.
“Wannan sanarwar tana da mahimmanci don tura isassun matakan tsaro da tabbatar da amincin jama’a da kuma hana bala’o’in da za a iya gujewa.
“Rashin bin wannan umarnin zai sa masu shirya taron su kasance da alhakin duk wani abu da ya faru ko asarar rai sakamakon sakaci,” in ji shi.
Shaidun gani da ido
Shaidun gani da ido sun ce turmutsutsun ya faru ne tsakanin karfe 7 na safe zuwa 8 na safe yayin da jama’a suka yi ta tururuwa domin karbar kayayyakin.
Turmutsutsun Okija
Majiyoyi a taron Okija sun shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa wannan bala’in ya faru ne sakamakon kwadayi da yunwar wadanda suka amfana. An gano cewa akwai isassun buhunan shinkafa ga daruruwan mazauna wurin da suka yi tururuwa zuwa wurin taron, amma mabukata sun rinjayi masu shirya taron, inda suka kutsa domi diban kaya da yawa, lamarin da ya sa aka kasa shawo kan lamarin.
Anambara
A Anambra kuwa, shaidun gani da ido sun ce mazauna yankin da dama sun suma yayin da wasu kuma suka fadi aka tattake su. Hakazalika, wasu buhunan shinkafa sun fado mutanen a lokacin da suka zame daga hannun wadanda ke gaggawar dauka.
Da take bayyana yadda lamarin ya faru, wata shaidar gani da ido, Misis Maria Okonkwo, ta ce, “Mutane sun taru da yawa, kuma wasu nakara tururuwa zuwa wurin domin karbar buhunan shinkafa a lokacin da wurin ya rikice aka fara ihu. Masu shirya taron kuma sun shagaltu da kokarin shawo kan lamarin, amma ina, babu abin da za su iya yi domin taron jama’ar ya fi karfinsu.
“Wasu mutane ne suka fara faduwa kasa, jama’a da dama sun tattake su, lamarin da ya kai ga mutuwarsu.
“Ba zan iya cewa ga adadin mutanen da suka mutu ba, amma zai iya zama kusan 10 ko 13, amma wadanda suka jikkata kam sun fi 30. Kimanin shida an dauke su sume,” in ji ta.
Kokarin zuwa wajen masu shirya taron ya ci tura domin babu daya daga cikinsu da ya dauki wayarsa.
Da yake mayar da martani kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra, Tochikwu Ikenga, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai cewa, jami’an ‘yansandan jihar sun kwace ikon wurin a Okija.
“Bayanin farko sun nuna cewa wani sanannen mai raba tallafi daga al’ummar Okija, a cikin jadawalinsa na shekara, yana raba wasu abubuwan jin dadi ga al’umma don ba da tallafi ga marasa galihu.
Sai dai abin takaicin shi ne, kafin a fara taron, mutanen da ba za a iya sarrafa su ba sun mamaye wurin taron, lamarin da ya haifar da turmutsitsi.
Sai dai bai bayyana adadin wadanda suka mutu ba, amma LEADERSHIP Sunday ta samu labarin cewa 19 ne suka mutu a wannan hatsarin.
Gwamnatin Anambra ta zargi masu shirya taron, tsofaffin shugabannin ‘yansanda, da wasu suna ba da mafita
A halin da ake ciki, kwamishinan yada labarai na jihar Anambra, Cif Law Mefor, ya bayyana bakin cikinsa dangane da wannan mummunan lamari.
Mefor ya dora alhakin lamarin a kan rashin tsari da masu shirya rabon abinci suka yi.
“Matsalar ita ce mutanenmu ba sa daraja tsaro yayin yin wani abu. Kamata ya yi masu shirya taron su nemi tsaro ta yadda za a tura jami’an ‘yansanda domin kula da jama’a.
“Idan da akwai ‘yan sanda a wajen taron, ya kamata su tabbatar kowa ya yi jerin gwano ya je daukar shinkafa daya bayan daya,” in ji Onyekonwu.
Okpe ya ce hanya mafi dacewa ta raba kayan agajin ita ce ta kungiyoyin kwadago da masu unguwanni, ba tara mutane da yawa wuri guda ba.
Ya ce, “Lokacin da nake DPO (Dibisional Police Officer) a Otukpa a Jihar Kogi, wani attajiri a wurin ya zo wurina ya ce in aika masa da jami’ai, yana so ya raba wa jama’arsa kayan abinci. Na ce masa, a’a. Na ba shi shawarar da ya je ya ba shugabannin kauyukan wadannan kayan. Kuma a bar shi ya je kowane kauye daga baya ya dauki shawarata ya yi aiki da ita.
An rarraba kayayyakin cikin lumana ga wadanda suka amfana. Don haka, babu bukatar tara sama da mutane 100, ko 1,000, ko 5,000 da kuma sama da mutane 1000,000 a wuri guda don raba abubuwan jin kai da su. Turmitsutus tabbas zai faru,” a cewar Okpe.
A ranar 18 ga watan Disamba, 2024, wani mummunan lamari ya faru a garin Ibadan ta Jihar Oyo, inda wani turmutsutsu a wurin baje kolin yara ya yi sanadiyar mutuwar akalla yara 35 tare da jikkata wasu da dama.
‘yan Nijeriya 213 ne suka hallaka a shekara 11 sanadiyyar turmutsutsu
A kalla ‘yan Nijeriya 213 ne suka rasa rayukansu a sanadin turmutsutsu cikin shekaru 11 da suka gabata, kamar yadda bincike da Daily Trust ya nuna.
Yawancin hakan ta faru ne a lokacin da rabon kayan abinci.
Haka zalika an samu irin wannan turmutsutsu a lokacin daukar ma’aikata da ayyukan addini. A cikin kwanaki shida da suka gabata, turmutsitsin da aka yi a lokacin rabon abinci ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 72 a garin Ibadan na jihar Oyo; Al’ummar Okija, Jihar Anambra da Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.
Kimanin yara 40 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsutsu a makarantar sakandaren Islamiyya dake Bashorun, Ibadan, a ranar Larabar da ta gabata, yayin wani bajekoli da wata tsohuwar sarauniyar Ooni na Ife, Naomi Shikemi ta shirya.
Wata mahaifiyar daya daga cikin wadanda turmutsutsun ya rutsa da su a Ibadan, Misis Oniyide, ta ce: “Ban san cewa wani mutum yana raba wani abu ba, ‘yata mai shekaru 10, Aina, ba ta gaya mani ba, babu wanda ya gaya min. Ta tafi talla kamar yadda ta saba kowace safiya, mun tsinci gawarta a daya daga cikin asibitocin da daddare.”